in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yunwa na iya sanya mutane saurin yin fushi
2014-07-21 14:00:04 cri
Wani bincike ya nuna muhimmancin kula da yawan sukarin da ke cikin jini, ga wanda kan takali uwar gidansa, ko wadda ta kan takala mijinta, duba da cewa karancin sukari a cikin jini na iya sanya mutum saurin hasala.

Jaridar kwalejin nazarin kimiyyar kasar Amurka ta PNAS ce ta gabatar da sakamakon wani nazari game da wannan batu a 'yan kwanakin baya, inda binciken ya nuna cewa saukar sukari a cikin jini kan sanya mutum saurin yin fushi, lamarin da ka iya sanya daya daga ma'aurta takalar abokin zaman sa.

A cewar binciken idan sukarin da ke cikin jinin mutum ya sauka, hakan na sanya shi jin yunwa. Kuma kamar yadda wani karin magana na Turanci ke cewa "mayunwaci na tare da bacin rai", hakan na iya haddasa mutun ya kasance cikin yanayi na fushi da bacin rai ya yin da ya fada cikin yanayi na karancin sukari a cikin jininsa.

Farfesa Brad Bushman na jami'ar Ohio dake kasar Amurka, wanda ke kula da nazarin ya yi bayanin cewa, nazarin ya bayyana wata matsala ta yau da kullum a tsakanin ma'aurata wadda a kan kauda kai daga gare ta, ta saukar sukari cikin jinni, wadda ke haifar da yunwa, sa'an nan yunwa ita kuma kan haddasa cacar baki, da fada, ta yadda hakan ka iya haddasa tashin hankali a tsakanin iyalai.

Wata tawagar manazarta da ke karkashin shugabancin Brad Bushman, ta yi bincike kan yawan sukarin dake jinin ma'aurata 107 kafin karin kumallo a ko wace rana, da kuma kafin shiga barci a daren ko wace rana. Ta kuma yi bincike kan yadda ma'auratan sukan yi fushi da juna, inda masu nazarin suka ba ma'auratan wata 'yar tsana wadda ke alamta abokan zaman su, da kuma wasu allurai guda 50, aka kuma bukaci ma'auratan da su rika soka allura guda jikin 'yar tsanansu a duk lokacin da suka yi fushi da abokan zaman su, wato da nufin auna yawan fushin da suke yi da juna.

Daga baya kuma masu binciken sun bukaci ma'auratan da su yi wasa da junan su ta na'ura mai kwakwalwa, kuma wadanda suka samu nasara a wasan za su aika da wata irin kara ga wadanda suka sha kaye, wadanda suka samu nasara na iya yanke shawara kan yadda karar za ta kasancewa, wajen girmanta ko kankanta, da tsahon ta ko gajartar ta. Har wa yau an sanar da wadannan ma'aurata cewa, 'yan takaran da suka yi wasa da su ta cikin wasan na'urar mai kwakwalwa abokan zaman su ne.

Manazartan sun gano cewa, mutanen da yawan sukarin da ke jininsu ya sauka sun sanya allurai da dama a jikin 'yar tsanar su, matakin da ya alamta yawan fushi da suke yi da ma'auratansu, kana kuma suna son wadanda suka sha kaye a cikin wasan da suka yi da na'ura mai kwakwalwa su ji babbar kara mai tsaho, lamarin da ya nuna cewa, watakila saukar sukurin dake cikin jinin su na haifar da saurin fushi.

Furfesa Brad Bushman ya yi karin bayani da cewa, mutane na bukatar yin amfani da karfi wajen kai zuciya nesa, da kaucewa yin fada da sauran mutane. Su na kuma samun irin wannan karfi ne daga sukurin da ke cikin jininsu, saboda kwakwalwasu kan yi aiki yadda ya kamata ta hanyar amfani da yawan sukarin. Farfesan ya kuma ba da shawarar cewa, ya fi kyau a ci isasshen abinci kafin a tattauna wasu batutuwa masu sarkakiyya tare da abokan zama. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China