Ina mai farin cikin shaida muku cewa, a ranar talata 08 ga watan Yuli shekara ta 2014, na samu muhimmiyar mujallar turanci da ake bugawa a kasar Sin(china Review) wadda malama Fatima Liu ta aiko mun. Babu shakka, na kara samun ilmi mai yawa a zahiri adangane da hakikanin abubuwan dake faruwa a fagen siyasar kasar Sin da ma na sauran kasashe, na kuma yi amanna cewa, kasar Sin kasa da ta ginu bisa adalci idan muka yi la'akari da shugabanni masu nagarta da adalci da Sin ta dace da su tun farkon kafuwar kasar Sin, lamarin da ya kara ingiza bunkasuwar kasar Sin cikin kankanin lokaci kuma cikin lumana. Matakan da kasar Sin ke aiwatarwa fiye da shekaru 50 da suka gabata na kiyaye zaman lafiya da martaba kasashe makwabta da sauran kasashen duniya , ya kara tabbatar da matsayin kasar Sin na martaba hakkin kasa da kasa. To, yanzu ke nan, Kasar Sin ta kasance wata muhimmiyar kasa daya tilo a duniya, wajen kin jinin haddasa yake-yake dake sabbaba malalar jinin al'ummar duniya.Ya zama wajibi, sauran kasashen duniya su gaggauta yaba wa kasar Sin da al'ummarta Sinawa masu akidar zaman lafiya da zaman cude-ni-in-cude-ka. A cikin mujallar ta china Review, na karanta irin muhimman matakan da gwamnatin jama'ar Sin ke dauka bisa aniyar sabbin shugabannin kasar Sin na murkushe muguwar dabi'ar cin hanci da wasu bara-gurbin masu rike da mukamai a gwamnatin kasar Sin ke yi loto-loto a kasar Sin. dud da cewar, ba safai ake samun wani ko wasu da laifin cin amanar kasa ba a kasar Sin, muna iya yaba wa gwamnatin jam'iyar kwaminist ta kasar Sin karkashin jagoranci shugaban kasar Sin malam Xi Jinping, bisa kokarinsu na iya cin nasarar dakile yaduwar aiyukan cin amanar kasa daga shekarun 2013-2014 inda aka samu nasarar yanke hukunci akan manyan jami'an gwamnatin kasar Sin su 2 wato, Bo Xilai da Xu Caihou. Tabbas wannan muhimmiyar nasara ce ga aniyar gwamnatin kwaminista ta kasar Sin na korar aikata laifukan cin hanci da karbar rashawa a kasar Sin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban cri Hausa listeners club na jihar Yobe, Nigeria.