in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yancin mata na da muhimmanci
2013-12-21 15:48:37 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya a nan birnin Kano. Bayan haka, na saurari shirinku mai farin jini na 'Gani Ya Kori Ji' wanda Malamai Ibrahim Yaya, Mamman Ada da Saminu Alasan suka gabatar mana jiya 18 ga wata.

Hakika, wannan shiri ya tattauna kan batu dake da muhimmancin gaske a wannan zamani da muke ciki, wato batun cin zarafin iyayenmu mata. Koda yake, batun cin zarafin mata ba wani sabon al'amari bane sakamakon yadda aka dade ana cin zarafin matan a fadin duniyar nan ta fuskoki da dama da ya hadar da mafi munin cin zarafi wato fyade musamman yayin yake-yake, da tilasta wa mata shiga karuwanci, da shan duka a hannun wasu mazajen aure, da dai sauransu. Duk da cewa, hukumomin dake fafutukar kare 'yancin bil Adam da sauran kungiyoyin mata sun dade suna yaki da wannan mummunar dabi'a ta cin zarafin mata, amma har yanzu za a iya cewa matsalar na ci gaba da fadada ne, sakamakon yadda lamarin a halin yanzu ya dauki sabon salo ta yadda ake samun rahotannin yi wa yara mata fyade ko tilasta musu shiga karuwanci.

Abu mafi muhimmanci a nan shi ne, ya kamata MDD bisa taimako da kulawar kungiyoyin fafutuka ta samar da wata tsayayyiyar doka ko wani hukunci na bai daya ga duk mutumin da aka samu da laifin aikata fyade ko wani nau'in cin zarafin mace a duk duniya. Wannan ko shakka babu zai taimaka wajen dakile wannan muguwar dabi'a ta cin zarafin mata. Ban da wannan, yanka wa duk mutumin da aka samu da laifin cin zarafin mata tara ta kudi mai yawa zai iya taimakawa wajen rage aukuwar matsalar.

Dangane da haka, batun kare 'yancin mata wani lamari ne da ya shafi kowa, sakamakon yadda ake samun rahotannin cin zarafin mata har a kasashen da suke da ci gaba. Saboda haka, kowa zai iya ba da tasa gudunmawa daidai gwargwado ta hanyar bayar da shawara ga mai cin zarafin ko sanar da kungiyoyin kare 'yancin mata ko kuma sanar da hukuma mafi kusa don gaggauta kawo dauki ga matar da matsalar ta shafa.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China