in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taya kasar Sin murnar samin nasarar jefa kumbo mai lamba Chang'e-3
2013-12-18 09:54:44 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan kunanan lafiya.

Bayan a mamadin 'yan kungiyar Great Wall ina taya kasar samin nasarar zama kasa ta 3 wacce ta harba kumbo zuwa duniyar wata, lallai wannan babbar nasara ce. Muna fatan jefa wannan kumbo zai kuma samarwa kasar SIN nasara sosai.

Badda haka na ji dadin shirye-shiryenku na wannan lokuta dafarko ranar 10/12/13 hirarku da A. Bamanga Tukur lokacin ziyararsa, inafatan koyin dayace zaiyi ga JKS zai aikata, haka kuma ranar 07/12/13 shirinku na kiwon lafiya wanda kukayi bayani akan tarin tibi lallai wannan mugun ciwo, kuma mun karu sosai akan wannan bayani.

Akarshe naji dadin shirinku na gani ya kori ji akan soyayyar matasan Beijing lallai nayi murnar jin za'a kara samar da wasu wasanni masu ilimantarwa kamar wannan. Sannan shirinku na jiya na inbaku yasa na jinjinawa Malama Wan mai cibiyar samar da aikinyi na gida da raino, a gaskiya irin wannan mata ake bukata domin ta ceci rayuwar al'umma sosai mata.

Inai muku fatan alheri.

Wassalam,

Abdulkadir Ibrahim,

Shugaban,

G.C.L.C, Kano.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China