in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likita Wang Zhenchang ya ba da gudummawa sosai wajen karfafa dankon zumunci tsakanin Sin da Guinea
2015-03-24 08:19:38 cri

Amma bayan da aka kafa rukunin likitocin, kafin tashinsu zuwa kasar Guinea, cutar Ebola ta barke a yammacin nahiyar Afirka, ciki hadda kasar Guinea wadda cutar tafi yiwa illa. A cikin wannan hali, ana mai da hankali ga batun ko wannan rukunin likitoci zai tashi zuwa Guinea cikin lokaci ko a'a. Wang Zhenchang kuma ya ba da amsa ba tare da bata lokaci ba, ya ce, "A lokacin, an fara janye jari, da mutanen Sin dake zama a wuri, da ma'aikatan Sin dake aiki a wurin daga kasashen dake yankuna masu fama da cutar Ebola a yammacin nahiyar Afirka. A sabili da haka, mun fuskanci babbar matsala, wato idan ba mu je ba, rukunin likitoci na baya ba zai iya komawa gida ba. Wannan ne tsarin kasa, shi ya sa dole ne wani rukunin likitocin Sin ya ci gaba da aiki a wurin a wancan lokaci."

A ranar 16 ga watan Agustar bara, a karkashin jagorancin Wang Zhenchang, rukunin likitocin da Sin ta tura zuwa Guinea karo na 24 ya isa kasar Guinea, wanda kuma ke kunshe da membobi 10. Kashe gari kuma suka fara aikinsu yadda ya kamata. A cikin wannan muhimmin lokaci, baya ga samarwa fararen hular Guinea fasahohi da kayayyakin aikin jiyya ga cutar Ebola da zuwan ma'aikatan ya haifar, a hannu guda kuma ya kara kwarin gwiwar jama'ar kasar game da dakile cutar Ebola. Wang Zhenchang ya bayyana cewa, "A ganina, abin dake gaban komai shi ne daidai halin da ake ciki. Hakan ya kara kwarin gwiwar kowane mutum dake kasar Guinea, ciki har da shugaban kasa da asibitocin kasar. A sabili da haka, dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kara samun kyautatuwa."

Ban da haka, yaduwar cutar Ebola ta yi babbar illa ga rayuwar mutanen Sin dake zama a Guinea, da ma'aikatan kamfanonin Sin a Guinea. Amma zuwan rukunin likitocin Sin a karkashin jagorancin Wang Zhenchang ya kwantar da hankalinsu. Wang ya ce, "Zuwanmu ya yi tasiri sosai ga kamfanonin Sin a Guinea. Sabo da a ganinsu, yanzu suna iya dogaro da mu. Za mu tabbatar da lafiyarsu yadda ya kamata, musamman ma a wannan lokaci na yaduwar cutar Ebola, likitoci masu kwarewa sosai sun zo daga birnin Beijing, suna kulawa da su a kasar Guinea. Dadin dadawa, mun kafa wani karamin asibiti a sansaninmu, inda muke ba da jiyya ga Sinawa cikin awoyi 24 ba tare da biyan ko kwabo daya ba."

A matsayinsa na shugaban rukunin, Wang Zhenchang ya zama mataimakin shugaban asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Guinea. Ban da gudanar da ayyukansa a wannan asibiti kuma, Wang yana horas da ma'aikata 'yan kasar a fannin kiwon lafiya, da sauran membobin rukunin. Irin wannan horo ba ma kawai ya rarraba fasahohin Sin masu daraja sosai na shawo kan cututtuka da kiwon lafiya ga jama'ar kasashen nahiyar Afirka ba, har ma ya zurfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. Wang ya kara da cewa, "Baki daya mun horar da mutane 1600, ciki har da ma'aikatan fadar shugaban kasar Guinea, da ma'aikatar tsaron kasa, da ma'aikatar harkokin waje ta Guinea da sauransu. Bayan horaswar, ra'ayinsu ya canza, za su dauki kwararran matakai a fannin kiwon lafiya a nan gaba. Hakan zai taimaka sosai wajen shawo kan cutar dake iya yaduwa a kasar a nan gaba."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China