in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likita Wang Zhenchang ya ba da gudummawa sosai wajen karfafa dankon zumunci tsakanin Sin da Guinea
2015-03-24 08:19:38 cri

Wang Zhenchang, shi ne mataimakin shugaban asibitin Youyi na Beijing na jami'ar horar da likitoci ta hedkwatar Sin, kana shugaban rukunin likitoci da Sin ta tura zuwa Guinea karo na 24, wanda ya dauki babban nauyin dake bisa wuyansa, na jagorantar rukunin ma'aikatan dake yanki da cutar Ebola a kasar Guinea, a yayin da wannan cuta ke yaduwa a yammacin nahiyar Afirka.

A matsayinsa na likita, ya ba da kulawa ga wadanda suka kamu da cututtuka, tare da horar da likitocin wurin bisa iyakacin kokarinsa, hakan ya aza tubali ga bunkasuwar sha'anin kiwon lafiya a kasar Guinea, tare da ba da babbar gudummawa ga karfafa dankon zumunci dake tsakanin Sin da kasar ta Guinea.

A karshen shekarar 2013, an ba da umurni ga asibitin Youyi na Beijing na kafa wani rukunin likitoci, wanda kuma Sin za ta tura zuwa Guinea a karo na 24. A sabili da haka, aka nada mista Wang a matsayin shugaban rukunin, domin gudanar da wannan aiki mai tsanaki yadda ya kamata.

"Mun kafa wannan rukunin likitoci ne a karshen shekarar 2013. Baki daya membobin rukunin 19 sun zo ne daga asibitin Youyi. Kuma wannan ne karo na farko da aka nada wani mataimakin shugaban asibitin Sin a matsayin shugaban rukunin likitoci da Sin ta tura zuwa kasashen waje. Ni ne na taki sa'ar zama shugaban wannan rukuni na farko."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China