in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhai Wenliang, shugaban tawagar ma'aikatan jinya na soja karo na 16 da kasar Sin ta tura kasar Zambia
2015-03-23 16:49:26 cri

An shaida cewa, kokarin da Zhai Wenliang ya yi tare da 'yan tawagarsa ya haifar da babban sakamako. A cikin shekara daya kacal, tawagar ta sa wadda ta tinkari mawuyacin hali na rashin na'urorin kiwon lafiya na zamani, da rashin isasshen ruwa da wutar lantarki, kana da hadarin kamuwa da cutar kanjamau, ta kammala ayyukan jinyar marasa lafiya a asibiti har karo 6200, da gudanar da bincike iri daban daban sama da sau 4100, da ba da jinya ga masu dauke da ciwuka fiye da sau 6000, da kuma duba marasa lafiya na hadin gwiwar likitoci fiye da sau 840.

Masu fama da ciwuka na wurin da yawa sun nuna yabo matuka game da kwarewar da kungiyar ba da jinya ta kasar Sin ta nuna, da hidima mai kyau da suka samar, ciki har da sakatariyar ministan tsaron kasar Zambia, Rose Salakatula. Madam Rose ta dade tana fama da ciwo a cinya, amma bayan ta samu jinya daga Zhai Wenliang, ta warke sarai. Tun daga lokacin, madam Rose ta kara nuna yabo sosai ga kwarewar likitocin kasar Sin.

A yayin da suke kokarin ayyukan ba da tallafi, a sa'i daya kuma Zhai Wenliang da 'yan tawagarsa sun yi amfani da sabbin fasahohi, don gudanar da wasu sabbin ayyukan, ta yadda suka kammala ayyuka a fannoni 15 da ba a taba aiwatarwa ba a wurin. Haka zalika sun yi kokarin horar da likitoci, da masu aikin jinya na kasar Zambia, inda ko wanensu ya horar da likitocin kasar Zambia 2 zuwa 4.

Bisa kokarin da suka yi, bayan da suka kammala ayyukansu na tallafi, ma'aikatar tsaron kasar Zambia ta ba su lambar yabo ta hadin kai tsakanin kasa da kasa a fannin tsaron kasa, wadda ke alamta zumuntar dake tsakanin kasashen Sin da Zambia.

Bayan ya koma kasar Sin, Zhai Wenliang ya rika lura da labarun dake fitowa daga kasar Zambia, ya kan kuma yi mu'amala tare da tsoffin ma'aikatansa na asibitin Maina Soko. Ya ce idan akwai dama, yana fatan sake komawa kasar Zambia, domin ganin wannan asibiti da ya taba aiki. (Bilkisu)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China