in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhai Wenliang, shugaban tawagar ma'aikatan jinya na soja karo na 16 da kasar Sin ta tura kasar Zambia
2015-03-23 16:49:26 cri

Idan ana son kammala wannan aiki yadda ya kamata, da farko akwai bukatar warware matsalar banbancin harsuna. Kafin su tashi, Zhai Wenliang ya gayyaci wani malami don koyar da dukkan 'yan tawagarsa Turanci. Bayan sun iso Zambia kuma, ya gayyaci ma'aikatansa biyu na kasar Zambia, don su rika tattaunawa da ma'aikata Sinawa, ta yadda 'yan tawagar suka sami fahimtar yaren jama'ar wurin, kuma suka samu damar shiga ayyukansu yadda ya kamata.

Haka zalika, kafin su tashi Zhai Wenliang ya san cewa, yanayin aikin jinya da kasar Zambia ke ciki ba ya da kyau, saboda haka, shi da 'yan kungiyarsa sun kara koyon ilmin likitanci, da kuma tattara magunguna da yawa. Yana fatan ban da fasahohin da suka kware a kan su, za kuma su iya hada kai tare da sauran likitoci domin gudanar da tiyata, da sauran ayyukan jinya.

Bayan sun isa kasar Zambia kuma, Zhai Wenliang ya gano cewa, sakamakon rashin kwarewa a fannin kiwon lafiya, da karancin na'urori, da magunguna, da yawa daga tallafin kasar Sin na magunguna, na ajiye a rumbun adana magani a maimakon amfani da su.

Saboda haka ne, Zhai Wenliang ya jagoranci 'yan tawagarsa zuwa dakin magunguna, da rumbun adana na'urori, da kuma dakunan gudanar da aikin tiyata na asibitin Maina Soko, inda suka yi gyare-gyare kan na'urori, kana suka sanya bayanai na Turanci kan dukkan magungunan gargajiyar kasar Sin. Ta yadda za a iya yin amfani da dukkan wadannan na'urori da magunguna.

Ban da wannan kuma, Zhai Wenliang ya gabatar da wani burin yin kirkire-kirkire ga 'yan tawagarsa, wato kowanensu bayan kamala ayyukansa, zai kara wani aiki na daban. Wannan burin ya sanya duk 'yan tawagar samun kwarin gwiwa wajen kammala ayyukan tallafi cikin nasara.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China