in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhai Wenliang, shugaban tawagar ma'aikatan jinya na soja karo na 16 da kasar Sin ta tura kasar Zambia
2015-03-23 16:49:26 cri

A shekarun 1980, bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Zambia, sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin sun soma ba da tallafi ga Babban Asibitin "Tri Service" na kasar Zambia. Tun daga shekarar 1984 har zuwa yanzu, kasar Sin ta turo tawagogi 18 da suka kunshi likitocin soja kusan 200 zuwa kasar ta Zambia, don samar da hidima a fannin aikin jinya, da kuma fasahohi. Zhai Wenliang, wanda ya fito daga asibiti na 175, na rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin, a matsayinsa na shugaban tawagar ba da jinya na soja karo na 16 da Sin ta turo a kasar Zambia, daga ranar 21 ga watan Janairun shekarar 2013 zuwa ranar 28 ga watan Janairun shekarar 2014, ya shugabanci ma'aikatansa wajen cimma cikakkiyar nasara kan ayyukansu a asibitin Maina Soko na kasar Zambia. Kokarin da suka yi ya samu yabo sosai daga majinyata, da Sinawa dake zaune a wurin, kana ya taka rawa wajen sada zumunci tsakanin kasashen biyu.

A watan Oktobar shekarar 2012, an baiwa asibiti na 175 na rundunar sojojin 'yantar da jama'a wani aiki na tallafawa kasar Zambia, Zhai Wenliang, wanda ya yi aiki a lokaci bai fahimci hakikanin yanayin da kasar Zambia ke ciki sosai ba a wancan lokaci, sai dai ya ji an ce, wannan wata kasar Afirka ce maras karfi a fannin kayayyakin more rayuwa. Amma, a matsayinsa na wani soja, ba tare da yin dari-dari ba ya karbi wannan nauyi na zama shugaban tawagar aikin jinya karo na 16.

Kasar Zambia tana kudu maso tsakiyar Afrika, kuma kasa ce mai yawan sauro, da yaduwar cutar kanjamau, da ta cizon sauro. Ban da wannan kuma, kasar na karancin isassun na'urorin jinya da magunguna, kuma jimilar likitocinta ba ta kai dubu 1 ba. Bisa wannan yanayin da kasar ke ciki, bayan ya karbi wannan aiki, ba tare da bata lokaci ba Zhai Wenliang ya jagora duk ma'aikatansa wajen gudanar da aikin share fage cikin gaggawa, a ganinsa sai da hakan za a iya tabbatar da gudanar da ayyukan ba da tallafin jinya a kasar yadda ya kamata.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China