in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Memban rukunin farko na likitocin kasar Sin da aka tura zuwa kasar Sudan ta Kudu Huang Fan
2015-03-23 16:46:22 cri

A ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2013, wato lokacin saura kwanaki fiye da 10 rukunin likitocin Sin ya komo kasar Sin, an samu tashe-tashen hankali mai tsanani a birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, an kuma samu rikice-rikice da suka janyo zubar da jini, tare da musayar wuta a kusa da wurin da rukunin likitocin Sin suke. Koda yake Huang Fan da abokan aikinsa sun san akwai hadari sosai wanda zai sanya iyalansu kara nuna damuwa don gane da su, kana ba a san yaushe ne za a kawo karshen rikicin ba, amma dukkansu sun zauna, domin a ganinsu ana kara bukatar gudummawar likitoci a yayin faruwar rikici. Huang Fan da abokan aikinsa sun ci gaba da gudanar da ayyukansu, da cimma nasarar bada jinya ga jama'ar Sudan ta Kudu, da Sinawa dake birnin su fiye da 10. Ayyukan rukunin likitocin Sin sun yi matukar burge ministan kiwon lafiya na kasar Sudan ta Kudu Riak Gai Kok, wanda hakan ya sanya shi bada lambar yabo ga mambobin rukunin, da yaba musu, bisa gudummawa kan sha'anin kiwon lafiya na kasar Sudan ta Kudu, kana ya kira su da sunan "manzonnin sada zumunta masu fararen riguna".

Huang Fan, matashin likitan fida ne, wanda ya bada gudummawa wajen sha'anin kiwon lafiya a kasar Sudan ta Kudu, ya cika alkawari na kasancewa wani likitan kasar Sin, wanda ya samu fasahohi da nasarori, yayin da yake gudanar da ayyukan gudummawar a Sudan ta Kudu. (Zainab)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China