in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Memban rukunin farko na likitocin kasar Sin da aka tura zuwa kasar Sudan ta Kudu Huang Fan
2015-03-23 16:46:22 cri

A karshen watan Disamba na shekarar 2012, Huang Fan ya yi ban kwana da iyayensa ya tashi zuwa Sudan ta Kudu. A matsayin membobin rukunin farko na likitocin Sin da aka tura zuwa Sudan ta Kudu, sun fuskanci matsaloli da dama. Da farko, likitoci da jama'a dake Sudan ta Kudu ba su da imani game da kwarewar likitocin Sin, kana ba su iya yin mu'amala sosai domin harsunansu sun bambanta, hakan ya kawo mawuyacin hali ga rukunin likitocin Sin wajen gudanar da ayyukansu a kasar Sudan ta Kudu.

Don haka, Huang Fan da abokan aikinsa sun shiga ayyukan bincike kan marasa lafiya, da bada jinya, da yin aikin tiyata tare da likitoci dake asibitin da suke aiki a kasar Sudan ta Kudu a kowace rana. Sannu a hankali kuma suka fara fahimtar juna. Kana Huang Fan da abokan aikinsa sun yi wasu ayyukan tiyata cikin nasara, wanda ya sa likitocin dake asibitin suka nuna yabo gare su.

A watan Yuni na shekarar 2013, wata mace mai suna Agnes Dim, daga yankin Yeyi na kasar Sudan ta Kudu ta kamu da ciwon kari, wanda girmansa ya yi kamar kwallon kwando a kan maman ta, kuma ciwon ya na kara tsanani. Rukunin likitocin Sin dake kasar Sudan ta Kudu ya karbi wannan maras lafiya, aka sanya Huang Fan da wani likita daban su yi aikin tiyatar cire mata karin. Yayin da ake yin aikin tiyatar, Huang Fan ya gano cewa, hanyoyin jini dake hade da karin suna da girma, kuma idan karin ya juya, za a lalata hanyoyin jini, wanda hakan zai sa ta zubar da jini nan da nan, kuma watakila hakan ya janyo rasuwar ta. Koda yake akwai babban hadari a aikin tiyatar, amma Huang Fan yana da fasahohi masu kyau da daidaita hanyoyin jini da cire karin cikin nasara.

Rukunin likitocin Sin dake kasar Sudan ta Kudu ya cimma nasarori da dama wajen bada jinya da yin aikin tiyata, ta haka aka kawar da damuwa da rashin karfin gwiwa da likitocin kasar suke nunawa membobin rukunin, kana sun jawo hankalin jama'ar dake kasar. Mutanen kasar da dama sun rika zuwa neman magani daga rukunin masu bada jinyar. Huang Fan ya yi amfani da dukkan lokacinsa wajen bada jinya ga marasa lafiya dake kasar.

A hakika dai, likitocin Sin da aka tura zuwa kasar Sudan ta Kudu sun fuskanci matsaloli masu tsanani da dama, yayin da suke gudanar da ayyuka, ban da yanayi mai zafi, akwai talauci, da cututtuka masu yaduwa, har ma da rikice-rikicen da sojoji ke fafatawa.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China