in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Memban rukunin farko na likitocin kasar Sin da aka tura zuwa kasar Sudan ta Kudu Huang Fan
2015-03-23 16:46:22 cri

Huang Fan likitan fida ne a asibitin farko na jami'ar koyon ilmin likitanci ta lardin Anhui, wanda yake da aure da 'yan tagwaye. Ya kuma halarci kasar Sudan ta Kudu wadda ke matsayin kasa mafi talauci a duniya, domin gudanar da ayyukan ba da jinya, ya warware matsaloli da dama, da gudanar da ayyukansa na sada zumunta a tsakanin Sin da Sudan ta Kudu, kana ya kiyaye gudanar da ayyuka yayin rikicin basasar kasar ke faruwa a kasar ta Sudan ta Kudu, tare da bada jinya ga marasa lafiya.

Huang Fan, memban tawagar ma'aikatan jiyya ne mafi karancin shekaru a rukunin farko na likitocin Sin da aka tura zuwa kasar Sudan ta Kudu. Kuma a ganin mutanen kasar Sudan ta Kudu, likita ne shi mai ban-al'ajabi.

A watan Yulin shekarar 2011 ne aka kafa jamhuriyyar kasar Sudan ta Kudu. Kuma Sin ta shirya tura rukunin farko na likitoci zuwa kasar Sudan ta Kudun a shekarar 2012. A lokacin, Huang Fan ya samu yaransa ba da jimawa ba, kana yana kula da mahaifansa, amma a matsayin wani likita, ya kamata ya dauki alhakin bada jinya, da taimakawa jama'a dake kasashe masu talauci wajen kawar da cututtuka. Don haka, ya tsaida kudurin yin rajista don shiga rukunin farko na likitocin Sin da aka tura zuwa Sudan ta Kudu.

Ya ce, shi matashi ne, yana bukatar samun fasahohi yayin da yake gudanar da ayyukan bada jinya a kasashen waje, kuma iyayensa za su fahimce shi, za kuma su nuna goyon baya gare shi.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China