in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Murmushin jakadiya mai aikin yaki da cutar Ebola---Wang Jing
2015-03-23 16:09:43 cri

Tun daga lokacin da ta fara aiki a kasar Guinea, Madam Wang tana cike da murmushi don faranta ran sauran mutane, kana ta yi ta taimakawa mutane, a ganinta, murmushi ke iya karfafa gwiwar sauran mutane. A watan Fabrairu na shekarar bana, tawagar ma'aikatan lafiyar sun ji dadin sabuwar shekarar kasar Sin a yanayin zafi na kasar Guinea, Wang Jing ta bayyana cewa,

"A cikin wadannan shekaru biyu, na rika yin musayar ra'ayi tare da likitoci da ma'aikatan jinya na kasar Guinea, ina fatan zan ba da taimako gare su. Kuma ina fatan kokarin da na yi zai ingiza aikin kula da majiyyata a kasar. Idan akwai dama, ina son komawa wannan wurin da nake aiki yanzu, a gaba ina fatan za a daga matsayin kiwon lafiya a kasar Guinea, ta yadda daukacin jama'ar kasar za su iya samun damar samun kula da lafiya yadda ya kamata."(Lami)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China