in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Murmushin jakadiya mai aikin yaki da cutar Ebola---Wang Jing
2015-03-23 16:09:43 cri

Wang Jing, ma'aikaciyar jinya ce a asibitin sada zumunta na birnin Beijing, dake karkashin shugabancin jami'ar koyon ilmin jinya ta hedkwatar kasar Sin. Tana kuma daya daga cikin 'yan tawagar ba da taimakon jinya ta 24, wadda kasar Sin ta tura zuwa kasar Guinea.

A watan Agusta na shekarar bara, a daidai lokacin da kasashen Afrika ke fama da cutar Ebola mai tsanani, Wang Jing ta ba da kai wajen shiga aikin taimakawa kasashen Afrika game da yaki da cutar Ebola, inda ta fara aikin ba da taimakon jinya a Afrika na tsawon shekaru biyu. A kasar Guinea, ta nuna wa mutane kwarewarta wajen aikin jinya da haye wahalhalu iri iri.

Kasar Guinea ta kasance a yankin yammacin nahiyar Afrika, yankin da ya sha fama da ciwon zazzabin cizon sauro, da zazzabin dake shafar kwakwalwa, da kuma ire-iren wadannan cututtuka dake yaduwa a yankuna masu zafi na duniya. Kana cutar Ebola da ta fara yaduwa daga shekarar 2014, ta mai da kasar yanki mafi fama da wannan cuta. A daidai lokacin da Wang Jing ta isa kasar, ta yi kokarin aiki ba dare ba rana. A yayin da take waiwaye game da haka, ta ce,

"Lokacin da na sauka kasar Guinea, ana cikin yanayin bazara, akwai zafi da danshi sosai. Muna bukatar fidda ababen dake yada cuta daga wurare, mu kan yi gumi cikin 'yan mintoci a sakamakon sanya tufafin rigakafi masu kauri, da daukar na'urori masu nauyi. Da farko ba mu da damar kawar da tasirin bambancin lokaci, mun fara aiki nan da nan, a ganina, hakan ya tabbatar da aniyarmu sosai."

Ban da aikin fidda ababen dake yada cuta daga wurare, Wang Jing da sauran membobin tawagar suna da nauyin gudanar da aikin jinya nan da nan. A cikin halin yaduwar cutar Ebola, tawagar ta samar da hidimar jinya ga ma'aikatan kamfannoni masu jarin kasar Sin, da Sinawa dake kasar wajen yaki da kuma kandagarkin cutar ta Ebola. Wang Jing ta bayyana cewa, sun karbi majiyyata da yawa dake bukatar ceto, dukkanin membobin tawagar sun yi iyakacin kokarinsu domin gudanar da aikin jinya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China