in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Murmushin jakadiya mai aikin yaki da cutar Ebola---Wang Jing
2015-03-23 16:09:43 cri

"Isowarmu na nuna babban goyon baya ga ma'aikatan kamfanoni masu jarin kasar Sin, a lokacin da suka kamu da cuta, suna zuwa wurinmu da farko. Suna kwantar da hankalinsu, sabo da muna can. Mun taba ba da jinya ga mutane biyu da suka yi fama da cuta mai tsanani, sun riga sun suma, a yayin da aka kai su tasharmu. A karkashin jagorancin shugaba da mataimakin shugaban tawagar, wasu likitocinmu sun gudanar da aikin ceto nan da nan, muna da dukkan na'urorin da muke bukata, a cikin wancan irin hali, mun kare rayukansu cikin nasara. Sannan, mun yi taro domin neman wata hanya mafi kyau ta ba da jinya gare su."

A sakamakon kokarin da muka yi, da kuma aikin yaki da cutar da mazauna wurin suka yi, an samu sassauci kan yaduwar cutar. Sannan, membobin tawagar sun shiga asibitin sada zumunta a tsakanin Sin da Guinea don yin hadin gwiwa da musayar ra'ayi tare da likitocin wurin. A matsayinta na ma'aikaciyar jinya, Wang Jing na yin bincike kan ko wane majiyyaci domin ganin ko yana dauke da cutar Ebola ko a'a, ta yadda za a kare rayukan membobin tawagar da likitoci, shi ya sa, ta fuskanci babbar barazana.

Sakamakon manyan ayyukan da ta fuskanta, da kuma karancin lokacin hutu da ingancin abinci, Wang Jing wadda a karon farko ta bar gida ta samu tasiri da matsin lamba kwarai, har wani lokaci ma ta yi fama da rashin lafiya. Amma duk da haka, ta rika murmushi da yin iyakacin kokarin gudanar da aikinta. Wanda hakan ya yi matukar burge shugaban asibitin sada zumunta tsakanin Sin da Guinea Fode Ibrahima Camara.

Game da hakan Camara ya ce,

"Ko da yake a lokacin da kasar Guinea ke fama da cutar Ebola mai tsanani, Madam Wang Jing ta ba da horaswa ga ma'aikatan asibiti, ta ba mu babban taimako a wannan fanni. Da isowarta, ta fara horar da ma'aikatanmu nan da nan, a matsayin ma'aikaciyar jinya ta tawagar kasar Sin, tana da babban aiki, kuma duk da cewar tana shan aiki sosai, mu kan gan ta cikin fara'a da murmushi, kuma mun gamsu da kwarewarta wajen aiki."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China