in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barkewar cutar Ebola ba za ta sanya Lu Hongzhou ja da baya ba
2015-03-23 15:07:50 cri

A lokacin da Lu Hongzhou ke tallafin Afrika, ya kan yi mu'amala da likitocin wurare a cibiyar yaki da cutar Ebola, kuma bisa goron gayyata da aka ba shi, ya kan halarci taron da aka saba yi game da nazarin masu kamuwa da cutar a kasar Saliyo, da shiga cikin aikin gyara ka'idoji don ba da aikin jinya gare su, haka kuma, bisa iznin da aka danka masa, ya fasara wadannan ka'idoji da ake bi zuwa Sinanci, don kungiyar likitocin Sin dake zuwa kasashen Afrika su duba.

Yayin da aka tabo maganar musabbabin tallafawa kasar Saliyo, Lu Hongzhou yana ganin, akwai babban alhakin likita dake bisa kansa.Ya ce, "Yanzu, duniyar da muke ciki ta yi kama da wani babban kauye, bai kamata mu ji dadin zama a kasar Sin da ke da nisa sosai ba. Idan aka gano cutar Ebola a Afrika, ya kamata a gaggauta zuwa domin ba da taimako."

Lu Hongzhou da sauran abokan aikinsa, sun ba da horo ga masu aikin jinya, da ma'aikatan kiwon lafiya da masu aikin sa kai a kasar, matakin da ya haifar da sakamako mai gamsarwa. Ayyukan da suka yi, sun samu yabo daga jami'an gwamnatin Saliyo, ciki har da shugaban kasar, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake wurin. Shi ma wakilin hukumar WHO da ke kasar Sin Bernhard Schwartlander, ya jinjinawa likitocin kasar Sin, da jami'an kiwon lafiyar kasar, ya ce, "Masu aikin jinya sun bar gidajensu, don tafiya zuwa Afrika wajen yaki da cutar Ebola, inda babu otel mai kyau, kuma suna cikin mawuyancin hali. Don haka sun zamo jarumai. Abin da ya fi dacewa shi ne a jinjinawa dukkanin wadannan jarumai da ke fagen daga wajen yaki da cutar."

Idan aka waiwaya baya, tun kusan tsawon kwanaki 65 ana yaki da cutar Ebola, wato game da tafiya zuwa Afrika dake da nisan kilomita dubu 14, Lu Hongzhou ya gaya mana cewa, "Mun sada zumunta da jama'ar wurin, kuma cikin tsawon watanni 2 da muke aiki a Afrika, mun gudanar da ayyuka yadda ya kamata.(Bako)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China