in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barkewar cutar Ebola ba za ta sanya Lu Hongzhou ja da baya ba
2015-03-23 15:07:50 cri

Bisa al'adun wurin, a yayin bikin jana'iza, ana taba gawar mutum. Sabo da cutar Ebola tana bazuwa ta hanyar musayar ruwan jiki, rabin masu kamuwa da cutar sun samu kwayoyin cutar ne ta hanyar taba gawawwakin wadanda suka kamu da cutar.

Lu Hongzhou ya ce, dalilin da ya sa cutar Ebola ta samu yaduwa a kasar shi ne, rikon sakainar kashi da jama'a suke nunawa game da cutar. Ta hanyar ba da horo gare su, zai iya sanya jama'a kara mai da hankali game da batun. Mr. Lu ya ce, "Mun taba ganin wani mutum mai dauke da cutar Ebola yana tafiya, ba zato ya fadi kuma ya mutu, amma mazaunan wurin ba su ji tsoro ba, ba su lura da wannan batu ba, wannan shi ne rashin sani. Sabo da haka, muna fata za a yi kokarin ilmantar da jama'a. A lokacin, mun yi wani tayi, wato fadakar da duk jama'a, don gaya musu asalin cutar, da matakan da za a dauka don magance ta. Ta haka za a iya hana yaduwar cutar."

Wadannan kwararru sun haye wahalhalu cikin mummunan yanayi, cikin kwanaki 3 kacal, sun bude wani kwas na horaswa. Bayan da suka fara ba da horo, Lu Hongzhou da sauran kwararru sun sha aiki a fagen daga, wajen yaki da cutar, don cimma nasarar horar da jama'a.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a duk tsawon kwanaki 65 da Lu Hongzhou ya yi yana aiki a kasar Saliyo, shi da sauran kwararru daga kasar Sin, sun horar da jama'a masu gudanar da sana'o'i daban daban kimanin 3000, wadanda suka fito daga birane da kauyuka dake yammacin kasar, wato inda cutar Ebola ta fi kamari. Yanzu, wadannan mutane sun zama wani babban ginshiki na yaki da cutar. Lv Shan, kwararre ne a kasar Sin, wanda ya je kasar Saliyo tare da Mr. Lu ya ce, fasahohin da Sin ta samu wajen yaki da cutar SARS, sun yi amfani ga kasar Saliyo wajen hana yaduwar cutar Ebola. Ya ce, "Fasahohin da Sin ta samu wajen yaki da cutar SARS, sun yi amfani ga kasar Saliyo. Yayin da muka je kasar, babu wasu alamu na fadakar da jama'a, ko tashoshin binciken lafiyar jiki da aka kafa. Bayan da muka fara fadakar da jama'a, da gudanar da aiki a wurin ne komai ya fara gudana yadda ya kamata."

A wurin da cutar Ebola ke yaduwa, yadda za a yi a tabbatar da tsaro ya zama wani babban batu dake gaban ko wane kwararre, shi ya sa, Lu Hongzhou da sauran abokan aikinsa, a hannu daya, suke tashi tsaye don daukar matakai game da sa ido, da kashe kwayoyin cuta, a daya hannun kuma, suna lura game da shirya matakan da su dace, idan an kamu da cutar, ya ce, "A lokacin, ko wane mako, akwai likitoci da suka kamu da cutar, kuma wasunsu sun fito ne daga Amurka, ko hukumar WHO, ko kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF, kuma wasu sun mutu. Amma a wannan lokaci ban gaya wa iyayena ba don kada su damu. Haka kuma, na kan yi tunawa idan na kamu da cutar, wane mataki zan dauka, wato na shirya ta ko wane fanni."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China