in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barkewar cutar Ebola ba za ta sanya Lu Hongzhou ja da baya ba
2015-03-23 15:07:50 cri

A bara, an sha fama da cutar Ebola a wasu kasashen dake yammacin Afrika, a matsayin kasar Saliyo na wadda ke sahun gaba wajen fama da cutar ta Ebola, kasar ta jawo hankalin jama'ar kasashen duniya matuka.

Don gane da hakan ne ma kwararre a fannin yaki da yaduwar cututtuka na kasar Sin Lu Hongzhou, da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya su 11 suka isa kasar, mai nisa daga kasar Sin.

Da sanyin safiyar ranar 9 ga watan Nuwanbar baran ne kuma, kungiyar ba da horo game da kiwon lafiya ta farko da Sin ta tura domin taimakawa Afrika ta tashi daga Beijing, ta kuma isa kasar Saliyo da ke yankin yammacin Afrika inda cutar Ebola ta yi katutu. Sabo da dakatar da sufuri da manyan kamfanonin jiragen sama suka yi zuwa kasar, tawagar ta Sin ta shafe awoyi sama da 30, tana canja jiragen sama har 4, kafin isa birnin Freetown, hedkwatar Saliyo.

Birnin Freetown, wanda shi ne hedkwatar Saliyo, kuma cibiyar kasuwanci ta kasar dake gabar tekun Atlantic, ya hadu da matsin lambar cutar Ebola, ga shi kuma kusan kashi 1 cikin 6 na jama'ar kasar suna zaune ne a wannan yanki.

Yayin da cutar ke yaduwa, sha'anin likitanci na wurin ya kusan rugurgujewa, ana bukatar taimako ruwa a jallo daga kasashen waje. A sa'i daya kuma, bayan da ake sake ginin birnin cikin shekaru da dama, an kasa warware matsalar shara dake addabar sa. Kwararre a fannin hana yaduwa cututtuka na Sin Cao Chunli wanda ya je Saliyo tare da Lu Hongzhou, ya ce, banda teku, duk ruwan da aka gani a kan hanya, akwai shara a ciki ke nan, an gurbata yanayi sosai a wurin. Ya ce, "Akwai shara sosai a kogin da muka gani, kuma akwai wari sosai, kuma duk hanyoyin da muka bi a kasar, daya suke a cikin wannan yanayi, akwai matukar hadarin sake bullar cutar.

Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayar, an ce, ya zuwa karshen watan Oktobar shekarar 2014, mutane sama da 13000 sun kamu da cutar Ebola, kuma mutane kimanin dubu 5 sun mutu.

A kasar Saliyo, akwai kungiyoyin ba da agaji na kasa da kasa, da na hukumar WHO, da ma sauran kungiyoyin horar da likitoci da dama. Bayan da kwararrun kasar Sin suka yi la'akari da yanayin da ake ciki a wurin, sun yanke shawarar ba da horo ga jama'ar wurin. Lu Hongzhou ya ce, "Kungiyar WHO ta mai da hankali game da horar da likitoci a wurin, yayin da mu, muka karkata hankalinmu game da horar da jama'a. Yaduwar cutar Ebola a asibitin ba ta da yawa, ya kamata a magance yaduwar cuta a tsakanin jama'a, musamman ma a yayin binne mamata, sabo da haka, a ganina, horon da muka ba da, ya taka muhimmiyar rawa a wannan fanni."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China