in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yu, wani likitan kasar Sin da ke ba da taimakon jiyya a kasar Saliyo
2015-03-23 09:08:51 cri

Kasar Saliyo tana daya daga cikin kasashen da ke fama da talauci a duniya, inda wasu jama'arta ba su da isasshen kudin ganin likita. Yayin da Wang Yu ya gamu da irin wadannan mutanen da suka kamu da cututtuka, ya kan yi iyakancin kokarinsa, domin rage yawan kudin da za su bukata, har ma ya kan ba su wasu magungunan kyauta. Game da wadanda ba su da kudin ganin likita, amma suna fama da cututtuka masu tsanani kuwa, Wang Yu ya kan biya kudin da ake bukata da kansa. Wang Yu ya kan ce, ceton mutane aiki ne na likita, ko suna da kudi ko babu, ya kamata a nuna girmamawa irin daya ga rayukansu.

A watan Mayu na shekarar bara, cutar Ebola ta barke a kasar Saliyo, don haka Wang Yu da abokan aikinsa sun fara aikin yaki da cutar. A farkon barkewar cutar, akwai dimbin mutane da suka je asibitin Kong Harman Road don ganin likita, ciki har da wadanda suka taba zuwa yankunan da ke fama da cutar Ebola. Kana sabo da babu tufafin ba da kariya a wancan lokaci, ba yadda za a yi sai 'yan kungiyar ba da taimakon jiyya na kasar Sin su sa safar hannu da hular rufe fuska, wanda hakan ya jefa su cikin hadari na kamuwa da cutar ta Ebola.

A ranar 22 ga watan Yulin bara, Wang Yu ya ba da jiyya ga wata mace mai shekaru 30, kuma ya yi mata bincike don tabbatar da ko ta kamu da cutar Ebola ko a'a. Wang Yu ya furta cewa, a wancan lokaci, bai yi tsammanin cewa, matar ta kamu da cutar Ebola ba. Kuma kafin wannan, ba a taba ba da jiyya ga wanda ya kamu da cutar ba a duk asibitin. Don haka ba a san cewa, ita ce mutumiyar farko da ta kamu da cutar Ebola a birnin Freetown ba. Amma a rana ta biyu, sakamakon bincike ya wuce tsammanin mutane, wato an tabbatar da cewa, ta kamu da cutar Ebola. A rana ta uku, matar ta mutu a kan hanyar kai ta zuwa asibitin killace mutanen da suka kamu da cutar.

Da jin wannan labarin, Wang Yu ya ce ya tsorata, kuma ya san cewa, duk wadanda suka taba tuntubar matar nan za su fuskanci babban hadari. Daga baya, an killace shi a dakinsa har na tsawon kwanaki 21. Bayan da aka tabbatar da lafiyarsa, Wang Yu ya fito sannan ya ci gaba da aikinsa na ba da jiyya ba tare da bata lokaci ba. A ganin Wang Yu, asibiti ya yi kama da fagen daga, likitoci fa sojoji ne. A matsayin wani soja, idan ya ji amon bindiga, dole ne zai nufi gaba don yaki da abokan gaba.

"A matsayinmu na likitoci, a cikin wannan mawuyacin hali na fama da cutar Ebola, dole ne mu yi aikin warkar da mutane a maimakon ja da baya". Abin da Wang Yu ya fada ke nan, wanda ya shaida kulawar da likitocin kasar Sin suka nunawa jama'ar Afirka. (Kande Gao)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China