in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yu, wani likitan kasar Sin da ke ba da taimakon jiyya a kasar Saliyo
2015-03-23 09:08:51 cri

A watan Afrilun shekarar 2013, Wang Yu ya tashi zuwa kasar Saliyo don kaddamar da aiki na tsawon shekaru biyu, a asibitin gwamnati na Kong Harman Road da ke birnin Freetown, babban birnin kasar Saliyo. Sakamakon yakin basasa da aka gwabza a kasar cikin shekaru da dama, an lalata muhimman ababen more rayuwa sosai, ciki har da tsarin kiwon lafiyar jama'a. A cikin wannan kasa da ke da mutane miliyan 6.1, yawan likitocin da suka yi rajista bai kai dari daya ba. Wang Yu ya bayyana cewa, ko da yake asibitin Kong Harman Road yana daya daga cikin asibitocin gwamnati mafi kyau a birnin Freetown, amma a kan fuskanci matsalolin karancin ruwa, da wutar lantarki. A wasu lokuta, wutar lantarki na katsewa yayin da suke yin tiyata, ba yadda za a yi sai dai a yi amfani da fitilu masu amfani da batir. A wasu lokuta, aikin tsaftace kayayyakin jiyya na zama wata babbar matsala sakamakon rashin ruwa.

Bugu da kari, sakamakon tsanantar yanayin kiwon lafiya, wasu cututtuka marasa tsanani su kan addabi mazauna wurin. Ganin haka, Wang Yu ya ce, "kudurina na zuwan Afirka ya yi daidai. Gaskiya dai, Afirka na bukatarmu, ya kamata mu yi iyakacin kokari don taimaka wa jama'ar Afirka."

Saboda kara fahimtar aikin ba da taimakon jiyya ga kasashen Afirka, Wang Yu ya kara nuna kuzari cikin aikinsa. Bisa labarin da aka samu, an ce, ban da kungiyar ba da taimakon jiyya ta kasar Sin da ke Saliyo, akwai likitoci biyu kawai da wasu nus-nus na kasar a asibitin Kong Harman Road. Hakan ya sa likitocin kasar Sin ke daukar babban nauyin aikin ba da jiyya, har ma su kan yi aiki na kwanaki shida a kowane mako.

A matsayinsa na likitan sassan jiki, yana matukar shan aiki. Ya kan lura da mutane kimanin 20 masu dauke da cututtuka a kowace rana. Wato ke nan ya ba da jiyya ga mutane fiye da 5000 a cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata. Kuma Wang Yu ya kan kula da kowanensu cikin tsanake, hakan ya sa ya kan zama likita na karshe dake gama aiki a kowace rana, har ma ya kan gaza cin abinci yadda ya kamata a wasu lokuta. Ko da yake ya kan sha aiki matuka, amma da ya gano gamsuwar da mutane marasa lafiya suke nunawa, Wang Yu ya ce, gajiyar da yake ji ba ta damunsa.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China