in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan wata 'yar kabilar Uyghur da wani dan kabilar Kirgiz a jihar Xinjiang
2011-07-19 20:44:46 cri

Madallah! Yanzu ga wani labari na daban, dangane da wani dan kabilar Kirgiz dake zaune a jihar Xinjiang. Sunansa Uruz Ulay, mai shekaru 56 a duniya. Yana zaune ne a kauyen Ayibulake dake gundumar Wuqia ta jihar Xinjiang, malam, ka san wannan wuri ne inda aka fi samun yawan abkuwar bala'in girgizar kasa. A cikin 'yan shekarun nan, a wannan yanki, a kan samu abkuwar bala'in girgizar kasa jefi-jefi.

A watan Oktoban shekara ta 2010, iyalan Uruz sun kaura zuwa sabon gidansa da lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin ya bada tallafin ginawa. Bari mu ji abun da Uruz Ulay ke cewa:

"In ba tare da tallafin da gwamnati da sauran yankunan kasar Sin suka bayar ba, ba zan yi kaura zuwa irin wannan sabon gida ba. Na gode matuka saboda manufar tallafawa jihar Xinjiang da gwamnati take aiwatarwa, ta yadda za mu samu damar jin dadin zaman rayuwa."

Ba ma kawai iyalan Uruz sun yi kaura zuwa sabon gida ba, har ma sun yi ban kwana da wani irin zaman rayuwarsu na da, wato kiwon dabbobi kawai, babu wuraren kwana. A halin yanzu, Uruz ya gamsu sosai ga kyautatuwar zaman rayuwarsa, har ma ya jagoranci wakilinmu zuwa sabon gidan da yake zaune. Matar Uruz Madam Tuhtub Junus tana dafa abinci ta hanyar yin amfani da iskar gas, inda ta gayawa wakilinmu cewa:

"Lokacin da muke da zama a tsohon gidanmu, muna dafa abinci ne ta hanyar yin amfani da kara da kashin shanu, gaskiya akwai wahala. Amma yanzu muna amfani da iskar gas domin dafa abinci da ruwa. A baya, ba mu samun isasshen ruwa mai tsabta, yanzu muna samun ruwan famfo mai tsabta."

Bugu da kari, wakilinmu ya yi hira tare da wani jami'in kula da ayyukan tallafawa yankin Kezilesu na kabilar Kirgiz dake jihar Xinjiang mai suna Wang Xianliang, inda ya ce, domin bada tabbacin samar da isasshen ruwa a wurin, lardin Jiangsu ya zuba Yuan sama da miliyan 5 a kokarin samar da tsaftataccen ruwa ga gidajen manoma sama da dubu 5. Har wa yau kuma, a shekarar da muke ciki, lardin Jiangsu ya zuba Yuan miliyan 38 a fannin kyautata na'urorin da ake amfani da su a cikin masana'antar samar da ruwan famfo a wurin.

Mista Wang Xianliang ya bayyana cewa:

"Na farko, za mu yi kokarin kara samar da ruwa. Na biyu, za mu yi amfani da fasahohin zamani domin kyautata ingancin ruwa, a kokarin bada tabbacin samar da ruwan sha mai tsabta ga mazauna wurin."

Sana'ar kiwon dabbobi muhimmiyar sana'a ce ga wadannan makiyayan kananan kabilu, musamman ma sana'ar kiwon tumaki. Uruz Ulay ya gayawa wakilinmu cewa, a halin yanzu, an kyautata muhallin kiwon dabbobi, da shirya wasu na'urori da kayayyakin zamani don kiwon tumaki, abun da ya sa suke kara nuna kyakkyawan fata ga zaman rayuwarsu a nan gaba.

Uruz Ulay ya bayyana cewa:

"A halin yanzu, yanayin aikinmu ya kara samun kyautatuwa. Mun gina sabbin filayen kiwon tumaki, haka kuma muna da karin lokaci don tafiyar da ayyukan cin rani a waje. A nan gaba, muna fatan kara samun kudi, ta yadda za mu kara jin dadi!"(Murtala)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China