in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan wata 'yar kabilar Uyghur da wani dan kabilar Kirgiz a jihar Xinjiang
2011-07-19 20:44:46 cri

Kwanan baya, wasu wakilan cibiyarmu wato cibiyar watsa labarai cikin harsunan kasashen yammacin Asiya da Afirka sun kai wata ziyara jihar Xinjiang, inda suka ruwaito mana rahotanni na musamman dangane da yaya zaman rayuwar mazauna wurin yake. A cikin shirinmu na wannan mako, bari in bayyanawa masu sauraro labarai biyu da suka shafi 'yan kananan kabilu biyu dake zaune a jihar, wato 'yar kabilar Uyghur mai suna Tursun Nishakhan, da wani dan kabilar Kirgiz mai suna Uruz Ulay.

A wani kauye mai suna Qiaka dake gundumar Hetian ta jihar Xinjiang, akwai wata cibiyar yin ado kan tufafi ta hanyar amfani da allura da zare. A cikin cibiyar, akwai wata 'yar kabilar Uyghur mai kula da ayyukan dinki, sunanta Tursun Nishakhan, mai shekaru 53 a duniya.

Yanzu mu ga menene Madam Tursun ta fada:

"Na fara dinka tufafi da kaina tun lokacin da nike da shekaru 12 da haihuwa. A wancan lokaci, na koyi fasahar dinki daga wani tsohon malami a birnin Hetian. A shekarar da ta gabata, an kafa wata cibiyar yin ado kan tufafi ta hanyar amfani da zare da allura a kauyenmu, kuma an ba mu horo da darussa a wannan fanni."

To, wadanne irin ayyuka ne mutane su kan yi a wannan cibiya? A nata bangaren, darektar ofishin kula da harkokin mata dake gundumar Hetian Madam Gehemanisha Sadik ta gayawa wakilinmu cewa:

"Yanzu akwai ma'aikata 140 wadanda suke aiki a wannan cibiya, kuma aikin da su kan yi a kowace rana shi ne samar da tufafin yara kanana da matasa. Yawan kudin da kowane ma'aikaci ya kan samu a kowace rana ya kai Yuan akalla 50, har ma wasu su kan samu Yuan sama da dari a kowace rana."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China