in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan wata 'yar kabilar Uyghur da wani dan kabilar Kirgiz a jihar Xinjiang
2011-07-19 20:44:46 cri

Yayin da wakilinmu ke hira tare da ita, wata yarinya ta je gurinsu. Sunanta Gulazhati Niyaz, mai shekaru 25 da haihuwa, wadda ta fara aiki a wannan cibiyar yin ado kan tufafi ta hanyar amfani da zare da allura bada jimawa ba. Ta gayawa wakilinmu cewa, a baya bata iya dinka tufafi ba, a shekarar da ta wuce, ta fara koyon fasahar dinki tare da Madam Tursun a cikin darussan da hukumar kauyensu ta shirya. Yanzu, Gulazhati Niyaz ta kan samu kudi sama da Yuan dari 6 a kowane wata. Yanzu bari mu ji menene wannan yarinya ke cewa:

"Yanzu ni kaina ina samun kudi, kuma zaman rayuwata yana kyautatuwa. A baya ina amfani ne da kudin mijina, amma yanzu ina samun kudi bisa karfina."

Har wa yau kuma, Madam Tursun Nishakhan ta gayawa wakilinmu cewa, ganin zaman rayuwarta na kara kyautatuwa, akwai abokanta mata da dama wadanda suka bayyana niyyarsu ta neman ayyukan yi a cibiyar yin ado kan tufafi ta hanyar amfani da zare da allura. Da ma wadannan mata 'yan kabilar Uyghur suna ayyukan gida ne kawai, shi ya sa kudin shigarsu ba shi da yawa. Yanzu matsakaicin kudin da su kan samu a kowane ya kai ya zarce Yuan dubu 1. Madam Tursun ta bayyana cewa:

"Wata aminiyata tana fama da ciwon kafafu, kuma tana shan wahala sosai a fannin zaman rayuwa. Amma bayan da ta fara aiki a wannan cibiya, ta halarci darussan horaswa da hukumar kauyenmu ta shirya, inda ta nakalci fasahohin dinka tufafi. A halin yanzu, zaman rayuwarta na samun kyautatuwa kwarai da gaske, kuma ta ji dadi sosai."

Haka kuma sauran birane ko kuma yankunan kasar Sin su ma suna bayar da taimako ga jihar Xinjiang. Alal misali, kungiyar hadin-gwiwar mata ta birnin Beijing ta dinga samar da tallafi ga ayyukan raya jihar Xinjiang. Darektar ofishin kula da harkokin mata dake gundumar Hetian Madam Gehemanisha Sadik:

"A bana, kungiyar hadin-gwiwar mata ta birnin Beijing ta zuba Yuan dubu 100, a kokarin gina wata cibiyar samar da horo a fannin yin ado kan tufafi ta hanyar amfani da zare da allura a gundumar Hetian, wadda za'a kammala gina ta a karshen wannan shekara."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China