in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manoman jihar Xinjiang suna jin dadin zaman rayuwarsu ta hanyar raya ayyujan gona bisa ilmin kimiyya
2011-07-19 17:41:16 cri

Y: To, Kande, masu rike da fasaha sun mai da hankali sosai kan wannan aiki domin amfana da mazauna wurin. Ina nuna musu babban yabo. Amma mutane su kan amince da wani abu bisa misali a maimakon bayani kawai. Yayin da wakilanmu suka aiki a jihar Xinjiang, ko sun ganam ma idanunsu yadda manoma yankin Kizilsu suka samu wadata?

K: Wakilanmu sun gaya mini cewa, yayin da suke yankin Kizilsu, sun gamu da wani matashi mai shekaru 26 a duniya. Sunansa Mamu Tean Bekri, yana daya daga cikin wadanda ke sa himma sosai kan ayyukan gona. An ce, a lokacin da, ya kan ci rani domin ciyar da iyalinsa. Tun daga shekarar bara da aka fara raya aikin shuka kayan lambu a rumfunan zamani a kauyensa, ya samu rumfuna guda 3. Kuma bisa jagorancin masu rike da fasaha, ya samun ilmin shuka barkono, tumatir, kwanana, da dai makamantansu. Sakamakon haka, zaman rayuwar gidansa ya samu kyautatuwa sosai. Mamu Tean Bekri ya wa wakiliyarmu cewa,

"Kafin na fara shuka kayayyakin lambu a cikin rumfunan zamani, ginamu ya fama da talauci sosai. Ba yadda za a yi, sai na kan je wuraren waje don ci rani, amma kudin da na samu kadan ne. A shekarar bara, gwamnatin ta ba ni rumfunan zamani 3, bayan shekara guda kawai, kudin da ko wane dan iyalina ya samu a ko wane wata ya karu daga kudin Sin Yuan 1500 zuwa Yuan2500."

Y: Madallah, raya ayyukan gona bisa ilmin kimiyya wata kyakkyawawr dabara ce wajen kyautata zaman rayuwar jama'a. Har yanzu, ina tunawa da cewa, yayin da nake jihar Xinjiang, na taba shiga wani gidan mazauna wurin, inda na ga akwai tabiliji da mota da sauran kayayaykin gida na zamani.Tun da kamar yadda ke fada dazu, wancan saurayi Mamu Tean Bekri ya samu wadata, ko gidansa ya yi kamar na taba gani a sauran wurare na jihar Xinjiang?

K: haka ne, wakilanmu sun gaya mini cewa, bayan da Mamu Tean Bekri ya kara samun kudin shiga, ya sayi talibijin da babur, zaman rayuwarsa ya samu kyautatuwa sosai. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, ban da karuwar yawan kudin shiga, yanzu 'yan iyalinsa suna ci kayayyakin lambun da suka shuka da kansu, ire-irensu kuma sun karu in an kwatanta da na da. Nurbiye Ismail, matar Bekri ta kuma gaya wa wakilanmu cewa,

"A lokacin da, ba yadda za a yi sai mu sayi kayan lambu da gari da nama a kasuwa, amma yanzu, kayayyakin lambu da muka shuka da kanmu suna iya biyan bukatunmu."

K: A hakika dai, a yanzu haka, kashi fiye da 80 na manoma na makiyaya da ke kauyen Suntag sun riga sun fara samun horaswa ta fuskar raya ayyukan gona irin na zamani. Kuma a yankin Kizilsu, akwai garuruwa da dama da suka raya ayyukan gona irin na zamani da shuka kayan lambu a cikin rumfunan zamani kamar yadda kauyen Suntag ke yi.


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China