in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manoman jihar Xinjiang suna jin dadin zaman rayuwarsu ta hanyar raya ayyujan gona bisa ilmin kimiyya
2011-07-19 17:41:16 cri

Y: Lallai, wannan wata kyakkyawar dabara ce. Kande, bayan da na dawo daga jihar Xinjiang a bara, ko da yaushe na kan mai da hankali kan labaru game da jihar. Kuma na samu labarin cewa, tun daga shekarar bara, lardin Jiangsu na shirya ware kudin Sin Yuan miliyan 100 ko fiye ga biranen Atushi da Aheqi da Wuqia na yankin Kizilsu daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2015, domin raya ayyukan gona irin na zamani da gayyatar kwararru zuwa wurin don ba da darussan shuke-shuke. Lallai wannan ya amfana wa manoma wurin sosai, ko ba haka ba Kande?

K: Gaskiyarka. A cikin hotunan da wakilanmu suka dauka a jihar Xinjiang, wasu sun burge ni kwarai da gaske, kuma a ganina su abun shaidu na taimakon da ake bai wa jihar Xinjing.

Y: Me keka gani a kan wadannan hotuna, Kande?

K: Wurin da aka nuna a kan hotunan, cibiyar gwaji ne na ayyukan gona da aka kafa a yankin Kizilsu, inda ake iya ganin cewa, rumfunan zamani na shuke-shuke na da matukar yawa, wadanda aka gina su ne a kan hamada da duwatsu, a cikinsu kuma, ana iya ganin kayayyakin lambu da ya'yan itatuwa iri iri masu ganye, wadanda har ma ba a iya gaskata da cewa, sun fito ne daga hamada da duwatsu.

Y: Lallai, abin mamaki ne kwarai. Mazauna yankin Kizilsu kuma sun samu alheri sosai sakamakon taimakon da aka bayar.

K: abin haka yake. A wadannan shekarun da suka gabata, ko da yaushe gwamnatin kasar Sin ta kan dora muhimmanci kan aikin tallafa wa jihar Xinjiang. Kuma Lardin Jiangsu shi ne ya kula da ci gaban yankin Kizilsu na kabilar Kirgiz. Yayin da Abduresul Imamu, wani jami'in kauyen Suntag na yankin ke zantawa da wakilanmu, ya furta cewa, yau da shekara guda da ta gabata, jami'an lardin Jiangsu sun shiga wannan yanki tare da kudaden gina rumfunan zamani na shuke-shuke, da kuma fasahohin shuke-shuke.

"A lokacin da, ba a gudanar da ayyukan gona a wurin ba, inda ba a iya samun gonaki ba sai dai hamada da duwatsu, har ma ba a iya samun manoma ba sai dai makiyaya kawai. Mazauna wurin ba su san fasaha da kimiyya ba, kuma ba su gaskata da su ba. Game da rumfunan zamani na shuke-shuke, ba a san kome ba. Amma bayan lardin Jiangsu ya fara samar da taimako ga wurinmu a watan Agusta na bara, an horar da mazauna a fannonin ayyukan gona da fasahar shuke-shuke da kiwon dabbobi."

Y: Lallai, an bai manoma taimako sosai wajen kyautata zamansu. Amma Kande, ina da wata tambya, wato game da makiyaya da suka saba da aikin kiwon dabbobi tun kakani-kakaninzu, ko za su saba da ayyukan gona?

K: E, wannan tambaya ita ma ta taba dame ni, har ma ina zaton cewa, makiyaya ba su iya saba da ayyukan gona cikin sauki ba, balle ma bari su gaskata cewa, za a iya samun girbi a kan hamada da duwatsu. Wannan matsala ta dami masu rike da fasaha na wurin sosai. Yayin da wakilanmu ke yi hira da wani mai rike da fasaha na kauyen Suntag, ya yi bayani kamar haka:

"Mu kan kai wasu mazauna marasa ilmi rumfunan zamani na shuke-shuke, domin su ganam ma idanunsu yadda sauran manoma ke yi gona, da kuma yin musayar ra'ayoyi tare da su, hakan ya samu kyakkyawan sakamako, bayan da su kammala wannan ziyarar, su kan nuna himma da kwazo kan ayyukan gona."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China