in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manoman jihar Xinjiang suna jin dadin zaman rayuwarsu ta hanyar raya ayyujan gona bisa ilmin kimiyya
2011-07-19 17:41:16 cri

Y: Kande, na samu labarin cewa, 90% na fadin yankin Kizilsu na kabilar Kirgiz na jihar Xinjiang duwatsu da kuma hamada ne. Idan aka ambaci hamada da duwatsu, a kan yi tsammani cewa, tabbas ne wannan wuri na fama da talauci sosai. Ko 'yan kabilar Kirgiz suna fuskantar da wadannan matsaloli?

K: Da ma na kan nuna musu damuwa kamar yadda kake zato. Amma bayan da na ga hotuna da wakilanmu wadanda suka ziyarci yanki a kwanan baya suka dauka kan yankin Kizilsu, na yi mamaki sosai, yankin na da yawan gonaki masu albarka, manoma wurin kuma suna jin dadin zaman rayuwarsu sosai.

Y: Me ya sa haka? Da ma an ji an ce, 'yan kabilar Kirgiz sun yi zamansu kamar mu Hausawa mu kan yi, wato su kan dogara bisa aikin kiwon dabbobi wajen zamansu. Yanzu sun fara aikin gona a maimakon kiwon dabbobi?

K: Ibrahim, ka san sakamakon karuwar yawan mutane, yanzu ciyayi na samun raguwa a ko wace shekara, don haka ba kawai makiyaya ba su iya kiwon dabbobi kamar yadda su kan yi a da ba, hatta ma muhallin halittu ya lalata sosai. Domin warware wannan matsala, ofishin kula da aikin tallafawa jihar Xinjiang na gwamnatin lardin Jiangsu wato garina ta fara ba da taimako ga jihar Xinjiang tun daga shekara ta 2010, wato sun shigar da fasahohin zamani na ayyukan gona, da kuma gina rumfunan zamani na raya ayyukan, a kokarin sa kaimi ga ci gaban ayyukan a yankin Kizilsu. Yayin da wakilanmu sun yi hira da mataimakin darektan wannan ofishi Zhang Jian, ya bayyana cewa,

"Galibin manoma masu kiwon dabbobi sun samu albashi kudin Sin Yuan 1500 kawai a kowace shekara, suna fama da talauci sosai. Shi ya sa, aiki mafi muhimmanci da muka yi shi ne kaurar da wadannan manoma masu kiwon dabbobi zuwa sauran wurare. Mun shigar da fasahohin aikin gona na zamani na lardin Jiangsu domin tallafa wa manoma wajen shuka 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu a rumfunan zamani, a sakamakon haka, manoma sun kara samun kudin shiga, haka kuma sun kafa muhallinsu sannu a hankali."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China