Wasu gwaje gwaje da na'urar Chang'e mai lamba-4 ta kasar Sin ta yi, a tsagin duniyar wata mafi nisa ya tabbatar da samuwar wasu bangori dake zube a wurin saukar na'urar. Wasu masanan kasar Sin sun wallafa sakamakon binciken a mujallar yanar gizo ta kimiyya a jiya Laraba.
Na'urar Chang'e mai lamba 4 ta sauka a doron duniyar wata sashen Von Karman cikin watan Janairun shekarar 2019, sa'an nan ta sauke na'urar binciken Yutu-2, domin nazartar sashin kwarin kudanci na bangare mafi nisa a duniyar watan. (Saminu Alhassan)