in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika kudurin yi wa hukumar WTO garambawul
2019-05-15 10:26:06 cri

Ma'aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce a shirye kasar take ta yi aiki da dukkan bangarori domin inganta yi wa hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO garambawul, ta yadda za ta fadada rawar da take takawa a fannin jagorantar tattalin arzikin duniya.

Majiyoyi daga sashen kula da harkokin WTO na ma'aikatar, sun ce Kasar Sin ta gabatar da kudurin na garambawul a hukumance ga hukumar a ranar 13 ga watan nan.

A cikin daftarin, kasar Sin ta yi nuni da batutuwa 4 da ke bukatar daukar gagaruman matakai, wadanda suka hada da; magance muhimman batutuwa dake barazana ga kasancewar hukumar da kara tasirin hukumar wajen jagorantar harkokin tattalin arzikin duniya da inganta karfin aikin hukumar da kuma kara shigar da tsarin huldar cinikayya tsakanin bangarori daban daban.

Kasar Sin ta ce yanayin tattalin azikin duniya na fuskantar sauye-sauye, yayin da batun dunkulewar tattalin arzikin duniya ke fuskantar koma baya, la'akari da yadda ake aiwatar da ra'ayi na kashin kai da kariyar cinikayya. Inda ta ce karfi da ingancin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban na fuskantar gagarumin kalubale.

Kafin nan, hukumar WTO na ta jan kafa game da tattauna batun garambawul da bukatar inganta yadda take gudanar da ayyukanta da tsarin cinikayya cikin adalci.

Duk da wadannan matsaloli, Kasar Sin na goyon bayan WTO ta aiwatar da gyare-gyare da suka kamata, domin warware rikicin da ake fuskanta da kuma cimma bukatun zamanin. Kasar Sin na girmama tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban da gina tattalin arzikin duniya a bayyane. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China