in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana rashin jin dadinta da matakin Amurka na kara mata haraji
2019-05-10 14:04:17 cri

Tawagar kasar Sin dake tattauna harkokin cinikayya da tattalin arziki da Amurka, ta bayyana rashin jin dadi game da matakin Amurka na karawa Sin harajin kaso 25 daga kaso 10, kan kayyayakinta da darajarsu ta kai dala biliyan 200.

Tawagar wacce yanzu haka ke birnin Washington domin zagaye na 11 na tattaunawarta da Amurka, ta ce matakin zai sanya kasar Sin ta mayar da martani.

Sanarwar da tawagar ta fitar, ta ce yayin da wannan zagayen tattaunawar ke gudana, kasar Sin na fatan bangarorin 2 za su yi kokarin warware matsalolin dake akwai ta hanyar hadin gwiwa da tuntubar juna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China