in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Amurka da Sin su yi aiki tare don karfafa dangantakarsu
2019-02-11 10:07:13 cri

Wani kwararre kan harkar tsara manufofi da wayar da kan al'umma na kasar Amurka, David Frestin, ya ce ya kamata masu tsara manufofi da 'yan kasuwa da malamai daga kasashen Amurka da Sin, su yi aiki tare wajen kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen.

Da yake halartar wani taron liyafa a ranar Asabar da yamma, wanda aka yi domin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, David Firestein, daraktan farko na cibiyar tsara manufofi da wayar da kan al'umma ta kasar Sin dake jami'ar Texas na birnin Austin, ya ce yanzu ne lokacin da ya dace a hadu a yi dukkan mai yiwuwa wajen karfafa dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin.

A cewar David Frestein, wanda kuma shi ne shugaba kana babban daraktan gidauniyar H.W Bush dake kula da dangantakar Sin da Amurka, akwai damarmakin a gaban shugabannin kasashen biyu na inganta kyakkywar alaka tsakanin kasashensu.

Ya kara da cewa, ana fuskantar kalubalen da ba a yi tsammani ba, haka kuma akwai damarmaki da ba a yi tsammani ba. Don haka ya ce, karkashin shugabancin kungiyoyin da suka halarci taron, za su iya samar da kyakkywan sauyi.

A nasa bangaren, Neil Bush, dan tsohon shugaban Amurka H.W Bush, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ya yi ammana mu'amala da musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu zai iya samar da sauyi mai kyau. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China