in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kama kafar Amurka a fannin kirkire kirkire
2019-04-09 13:16:17 cri

Bisa rahoton da cibiyar bincike da ba da shawarwari kan ayyukan fasaha ta Amurka wato Information Technology and Innovation Foundation (ITIF), kasar Sin tana kama kafar Amurka a fannin kirkire-kirkire.

Rahoton da aka fitar jiya, ya ce cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta yi kokarin cike tazarar dake tsakaninta da Amurka cikin sauri, kuma a yanzu, a wasu alamu sun nuna cewa ita ce ke gaba da Amurkar .

Ya ce a shekarar 2007, jarin kaso 33 cikin dari kasar Sin ta zuba kan irin wadancan ayyuka na fasaha, adadin da ya gaza wanda Amurka ta zuba. Sai dai ya zuwa shekarar 2017, kasar Sin ta yi kokarin cike tazarar ta hanyar kai wa kaso 76 cikin dari na matakin Amurka, kana ta zarce Tarayyar Turai.

Sassan gwamnatin kasar Sin sun kashe adadin kudi mai yawa kan bincike da samar da kayayyakin fasaha cikin alkaluman GDP fiye da Amurka, adadin da ya tashi daga kaso 84 cikin dari na matakin Amurka a shekarar 2007 zuwa kaso 119 cikin dari a shekarar 2017.

Har ila yau, yawan manyan kayayyakin fasaha da kasar Sin ta kera ya tashi daga kaso 30 cikin dari na shekarar 2006 zuwa kaso 77 cikin dari a shekarar 2016. Idan wannan ci gaban ya dore, kasar Sin za ta zarce Amurka a fannin samar da manyan kayayyakin fasaha ya zuwa shekarar 2020.

Rahoton ya ce daukar kasar Sin a matsayin mai kwaikwayon fasaha bai dace ba, domin za ta iya, kuma ma tana yin kirkire kirkiren. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China