in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hada-hadar kudi bisa amfani da katin banki na kasar Sin ya karu a lokacin hutun ranar ma'aikata
2019-05-06 09:09:13 cri
Kamfanin katin banki na hada-hadar kudi na UnionPay na kasar Sin, ya ce hada hadar kudi bisa amfani da katin ta karu yayin hutun kwanaki 4 na farkon watan Mayu, inda masu amfani da katin suka yi ta siyayya.

Jimilar hada-hadar kudi da aka yi bisa amfani da katin UnionPay ya kai yuan trilian 1.29, kwatankwacin dala biliyan 192, a tsakanin ranar 1 zuwa 4 ga watan Mayu, adadin da ya karu da kaso 42 a kullum daga na makamancin lokacin a bara.

Saboda karuwar ranekun hutun da kuma kyawun yanayi a galibin sassan kasar, bangarorin dake da alaka da yawon bude ido sun samu ci gaba sosai. Matsakaicin kudin da aka kashe kan kamfanonin shirya tafiye-tafiye da tikitin zuwa wurare masu kayatarwa ya karu da kusan kaso 60 a kan na bara, yayin da kudin da aka kashe kan otel-otel ya karu da kusan kaso 30, inda na gidajen abinci ya karu da kaso 20.

A bangaren tafiye-tafiye zuwa kasashen waje kuwa, wuraren shakatawa dake bunkasa yanzu kamar Turkiyya da Mauritius da Sweden, sun samu karuwar hada-hadar kudi bisa amfani da katin banki na UnionPay na kasar Sin. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China