in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzania ta kaddamar da dakin gwajin sinadarin uranium irin sa na farko a Afirka
2019-04-30 09:45:29 cri

Mahukunta a kasar Tanzania, sun kaddamar da dakin gwajin sinadarin uranium irin sa na farko a Afirka, a wani mataki na inganta sha'anin hakar ma'adanai, da gudanar da bincike da ya shafi bangaren.

An gina dakin gwajin ne a arewacin Safari dake birnin Arusha, fadar mulkin kasar, karkashin hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasar ko TAEC a takaice, aikin da ya kashe tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 4.3.

Da yake tsokaci jim kadan bayan kaddamar da dakin gwajin, firaministan kasar Kassim Majaliwa, ya ce Tanzania na kan gaba wajen kare manufofin hakar ma'adanai, da kula da sufurin sinadaran nukiliya, don haka kammala wannan dakin gwaji, zai zamo kari kan aniyar kasar ta tabbatar da cin gajiyar sa.

Ya ce, kawo yanzu, karkashin aikin sarrafa sinadarin uranium na kasar, an gano adadin da ya kai tan 59,000 na sinadarin, wanda shi ne adadi mafi yawa da aka taba ganowa a nahiyar Afirka.

Kassim Majaliwa ya ce, da wannan daki na gwaji karkashin hukumar TAEC, kasarsa na iya samar da hidimar gwajin sinadarin uranium ga dukkanin makwaftanta, a duk lokacin da ake da bukatar hakan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China