Taron dake gudana a birnin Dar-es Salaam, cibiyar kasuwancin kasar, ya hallara manyan sifetocin 'yan sandan kasashen Tanzaniya mai masaukin baki, da Kenya, da Rwanda da kuma Mozambique.
A jawabinsa na bude taron, babban sifeton 'yan sandan kasar Tanzaniya Simon Sirro, ya ce taron ya samar musu da wani dandali na bullo da matakan yaki da daukar kwararan tsari na doka kan laifukan da ake aikatawa a yankin da ma kasashensu.
Ya ce, sun dade suna aiki tare a fannoni daban-daban, suna kuma kokarin fito da wasu dabaru da za su taimaka wajen gano tare da magance manyan laifukkan da ake aikata a kan iyakokin kasashen.
A cewar Sirro, hadin gwiwar da suke yi, za ta taimaka wajen bankado maboyar wadanda ake zargi.(Ibrahim)