Kabudi wanda ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi ga kungiyar ma'aikata dake aiki a ma'aikatarsa a Dodoma, babbar birnin kasar, ya ce ya kamata jakadun kasar dake ketare su ba da muhimmanci wajen kulla alakar tattalin arziki da sauran kasashe. Daga nan sai ya bukaci ma'aikata dake aiki a ma'aikatarsa da su gudanar da ayyukansu bisa hakki da gaskiya, ta yadda za su yi goyayya a diflomasiyar kasa da kasa.
Ya ce, ya kamata jakadun kasar dake ketare su taimaka wajen zakulo masu sha'awar zuba jari, da masu yawon shakatawa zuwa kasar da nemo kasuwannin da za a rika sayar da amfanin gonan da ake nomawa a kasar.
A ranar 3 ga watan Maris din wannan shekara ce dai, shugaba John Magufuli na kasar Tanzaniya ya maye gurbin Augustine Mahiga da Kadubi a matsayin ministan harkokin waje. Yayin Mahiga ya zama sabon ministan harkokin shari'a da kundin tsarin mulkin kasa.(Ibrahim)