in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin shugabannin Sin da Djibouti
2019-04-28 16:24:08 cri

Shugaba kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Djibouti, Ismail Omar Guelleh, yau Lahadi a nan Beijing,

A yayin ganawar, shugaba Xi ya ce, kasar Sin na son hada kai da Djibouti wajen kara azama kan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka, a kokarin raya huldar abota a tsakanin kasashen 2, bisa manyan tsare-tsare. Xi Jinping ya ce, wajibi ne kasashen 2 su mara wa juna baya kan babbar moriyarsu da kuma manyan al'amura, da inganta tuntubar juna da taimakawa juna kan al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan Djibouti, wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar, da yin musayar fasahohin raya kasa da ita da karfafawa kamfanonin kasar Sin masu karfi gwiwar zuba jari da yin kasuwanci a kasar Djibouti.

A nasa bangaren kuma, shugaba Ismail Guelleh ya ce, ba a taba ganin irin shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya gabatar ba, yana mai cewa shawarar za ta sa kaimi kan hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar samun ci gaba. Kana za ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen kafa duniya mai kyakkyawar makoma ga kowa. Shugaban na Djibouti ya kara da cewa, suka mara dalili da wasu ke yi, ba za su sauya aniyar kasarsa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" ba, kuma ba za su sauya amincewar da kasarsa ta yi wa kasar Sin ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China