in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban DPRK ya isa Vladivostok don ganawa da takwaransa na Rasha
2019-04-25 09:58:22 cri

Babban kamfannin dillancin labaran kasar Koriya ta arewa, ya bayyana cewa, a jiya ne shugaban Koriya ta arewan Kim Jong Un, ya isa birnin Vladivostok dake yankin gabas mai nisa na kasar Rasha da misalin karfe 6 na yamma agaogon wurin, cikin wani jirgin kasa na musamman.

Rahotanni na cewa, Kim na shirin ganawa da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin yau Alhamis. Wannan dai shi ne, taron koli na farko da shugaba Kim zai yi da Putin, tun lokacin da ya zama shugaban kasar Koriya ta arewa a karshen shekarar 2011.

Ana saran shugabannin biyu, za su tattauna kan alakar dake tsakaninsu da batun kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China