Shugaban DPRK ya tashi daga Pyongyang zuwa Hanoi don halartar taron sake ganawa tsakanin DPRK da Amurka
Da yammacin jiya Asabar shugaban kasar Koriya ta arewa (DPRK), Kim Jong Un, ya tashi zuwa Hanoi babban birnin kasar Vietnam, domin halartar zagaye na biyu na taron kolin tattaunawa tsakanin DPRK da Amurka, kamfanin dillancin labaran kasar Koriyar (KCNA) ne ya bada rahoton a yau Lahadi.
Kim, zai gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump, a ranar 27 zuwa 28 ga watan Fabrairu. An gudanar da ganawar farko tsakanin shugabannin biyu ne a watan Yunin shekarar 2018 a kasar Singapore, inda ganawar ta haifar da kyakkyawan sakamako kan dangantaka a tsakanin kasashen biyu. (Ahmad Fagam)