Shugaba Trump ya sanar da hakan ne jiya Lahadi a shafinsa na Tweeter. Ya ce yana da imanin cewa,Koriya ta arewa tana da albarkatu, kuma wata rana za ta kasance babbar kasa a fannin tattalin arziki da harkokin kudi, kuma shugaba Kim Jong Un ya yarda da kalaman na Trump.
A jiya Lahadi ne dai jaridar Washington Post ta ba da labarin cewa, tsohon jakadan Amurka a Koriya ta Kudu Sung Kim ya tsallaka kasar Koriya ta arewa inda ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Koriya ta arewan Choe Son Hui game da shirye-shiryen taron kolin shugabannin kasashen biyu. (Ibrahim)