in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar dogo ta Abuja zuwa Kaduna ta kasar Najeriya na gudanar da aiki yadda ya kamata
2019-04-22 13:48:42 cri


Hanyar dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna a kasar Najeriya da kamfanin kasar Sin ya shimfida ya kuma samar da hidimar gudanarwa, ita ce hanyar dogo ta zamani dake na farko da kasar Sin ta shimfida a nahiyar Afirka. Ya zuwa yanzu, hanyar dogon ta shafe sama da kwanaki 1000 tana aiki yadda ya kamata, yawan fasinjiji da aka yi jigilarsu ya wuce miliyan 1.5, hakan ya kasance wata muhimmiyar nasara da kasashen Sin da Najeriya suka cimma kan hakikanin hadin kan samun nasara tare a fannin manyan kayayyakin more rayuwa.

Yanzu ga karin bayani da abokiyar aikinmu Bilkisu ta hada mana.

Hanyar dogo ta Abuja zuwa Kaduna, ita ce matakin farko na ayyukan zamanintar da hanyoyin dogo na kasar Najeriya, gwamnatin kasar Sin ce ta ba da rancen kudin gudanar da aikin kuma kamfanin CCECC na kasar Sin ne ya dauki nauyin ginawa tare kuma da samar da hidimar gudanarwa. Hanyar dogon ta hada Abuja, babban birnin kasar Najeriya, da kuma Kaduna, muhimmin gari a fannin masana'antu dake arewacin kasar, wadda tsawonta ya kai kilomita 186.5. Hanyar dogon ta soma aiki ne a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2016, a matsayinta na hanyar dogo ta zamani mai salon kasar Sin a dukkan fannoni da ta fi soma aiki a nahiyar Afirka, wadda kasar Sin ta samar da kudin aikin, kuma bisa ma'aunin kasar ta Sin, kuma kamfanin kasar Sin ya tsara ya kuma gina ta, tare kuma da samar da na'urori da goyon bayan gudanar da ita.

Kwanan baya, hukumar kula da zirga-zirgar hanyar dogo ta ma'aikatar sufuri ta kasar Najeriya ta ba da lambar yabo na "cika kwanaki 1000 da hanyar dogo ta Abuja zuwa Kaduna da fara aiki lami lafiya" ga kamfanin CCECC dake Najeriya, babban manajan hukumar kula da jiragen kasa ta kasar Najeriya, Adeola Adeokun ya bayyana a yayin bikin murnar cewa,

"Yau muna murnar cika kwanaki 1000 da hanyar dogo ta Abuja zuwa Kaduna ta fara aiki, a cikin wadannan kwanaki 1000 ba a samu ko wadanne irin hadarurruka ba, ciki har da rauni ko rasuwar fasinja, tafiye-tafiye, wannan wata babbar nasara ce, kamata ya yi mu yi godiya ga kamfanin CCECC kan goyon bayan da ya ba mu."

Bisa yanayin da kasar Najeriya ke ciki na rashin ci gaba wajen gudanar da ayyukan hanyar dogo, kamfanin CCECC yana tsayawa kan manufar "dunkulewar aikin gina da kuma gudanarwa", ya kuma samar da goyon baya ga hukumar kula da jiragen kasar Najeriya NRC a fannin fasahar gudanarwa, da ba da horo da inganta gudanarwar cinikayya ta hanyar dogon ta Abuja zuwa Kaduna. Babban manajan kamfanin CCECC dake Najeriya Jiang Yigao ya ce, a cikin kwanaki 1000 da soma aikin hanyar dogon, kamfaninsa da hukumar NRC sun hada kai don samar da hidimar tsaro, da inganta da kuma saukakawa fasinjoji, wannan ya sa suka samu yabo daga dukkan fannoni.

"Wannan wata muhimmiyar nasara da aka cimma kan hadin kai a tsakanin Sin da Najeriya, ita ce shawarar 'Ziri daya da hanya daya'. Nan gaba za a gina hanyoyin dogo masu yawa, jama'ar Najeriya da dama za su samu hidima mai cike da tsaro da sauki da kuma jin dadi."

Tun bayan kaddamar da hanyar dogo ta Abuja zuwa Kaduna, an rage yanayin cukoson hanyar mota a tsakanin birnin Abuja da yankin Naija da na Kaduna, wadda ta saukaka harkokin tafiye-tafiyen fasinjoji.

A cikin kusan shekaru uku da suka gabata, dan kasuwa Yusuf Mohammed ya kan dauki wannan jirgin dake tafiye-tafiye a tsakanin Abuja da Kaduna kusan ko wane mako, ya nuna yabo sosai kan hanyar,

"Yanzu ana samun sauye-sauye a hanyoyin zirga-zirga na fasinja da kayayyaki a kasar Najeriya, muna bukatar jiragen kasa da motoci masu yawa, ta yadda za su hada hedkwatocin jihohin kasarnu daban daban waje guda, gaskiya muna bukatar hanyoyin sufuri, ina fatan kasar Sin za ta ba mu goyon baya a wannan fannin."

Yanzu, an soma aikin shimfida hanyar dogo a tsakanin Legos da Ibadan, wanda ya kasance mataki na biyu na ayyukan zamanintar da hanyar dogo na kasar Najeriya, kuma kamfanin CCECC ne ke daukar nauyin ginawa, idan hanyar dogon ta soma aiki, za a samu saukin zirga-zirga a yankin kudu maso yammacin kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China