in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayin wata masaniyar harkokin Afirka ta kasar Sin kan zaben Najeriya
2019-02-15 19:50:03 cri

Gabannin zaben shugaban kasa a Nijeriya da zai gudana gobe Asabar, 'yan takarar shugabancin kasar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tabbatar da gudanar da zabukan kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.

Manyan 'yan takarar shugabancin kasar da suka hada da Muhammadu Buhari, shugaban kasar na yanzu, da dan takarar babbar jam'iyyar adawa Atiku Abubakar, na daga cikin wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, wadda ke nufin 'yan takarar za su ja hankalin jam'iyyu da magoya bayansu game da kauracewa duk wani abu da ka iya haifar da rikici yayin da kuma bayan zaben.

Dangane da haka ne wakilinmu gidan rediyo CRI ya tuntubi Dokta He Wenping, babbar mai bincike ta sashen nazarin harkokin yammacin Asiya da nahiyar Afrika ta cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin, inda ya fara da tambayarta, shin sanya hannu kan yarjejeniyar za ta taimakawa wajen kauracewa tashin fitina yayin da kuma bayan sanar da sakamakon zaben?

Dokta He ta ce:

"A ganina yarjejeniyar abu ne mai kyau, tun da yunkuri ne na 'yan takarar jam'iyya mai mulki da ta adawa, duk da ba zai bada tabbacin cewa ba za a samu tashin fitina ko kadan ba, a ganina za ta taka muhimmiyar rawa wajen rage tashin rikici."

Wakilinmu ya ci gaba da tambayarta, kusan dukkan manyan 'yan takarar wato Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar na cikin shekaru 70 ne, sannan suna da gogewa kan harkokin siyasa, amma mene ne bambancin dake tsakanin akidu da manufofinsu na siyasa?

He ta amsa cewa:

"A gaskiya babu wani gagarumin bambanci, dukkansu na alkawarin raya tattalin arziki ne da kyautata yanayin kasuwanci domin jan masu zuba jari na kasashen waje da yaki da cin hanci da ta'addanci. A ganina babu bambanci, wani muhimmin batun shi ne ra'ayin masu kada kuri'a. Duk da cewa jam'iyya mai mulki ta dade tana jan ragamar kasar, har yanzu tattalin arzikin kasar ba shi da karfi, duk da cewa kasa ce mafi karfin tattalin arziki a nahiyar. Sannan matakin rashin aikin yi ya karu, baya ga wasu batutuwa da suka kasa samun ingantuwa, don haka, wannan ne za a yi amfani da shi wajen tantance wanda zai ci nasara maimakon ra'ayoyi da taken jam'iyyu."

Wakilinmu ya tambaye ta, dan takarar jam'iyyar adawa, wato Atiku Abubakar, dan kasuwa ne da ya dade yana zuba jari a bangrori dama a kasar, ba kamar Buhari da ya mayar da hankali kan bangarorin gwamnati kuma yake tantama kan harkokin zuba jari ba, ya tambaye ta, a ganinta wannan zai kara masa kuri'a a zaben?

Madam He ta amsa cewa:

"Ba na jin wannan babban batu ne wajen kada masa kuri'a, duk da cewa dan kasuwa ne, ya san yadda zai samowa kamfanoninsa kudi, hakan na nufin ya san yadda zai inganta tattalin arzikin kasar, amma wannan wani abu ne daban, zama dan kasuwa ba zai taimaka masa wajen zama dan siyasa ba."

Wakilinmu ya ci gaba da tambaya, inda ya ce, kwanakin baya, Bill Gates ya ja hankalin shugabannin siyasa a kasar da su bar batun inganta ababen more rayuwa, su mayar da hankali kan amfana daga yawan al'ummar da kasar ke da ita, shin menene ra'ayinta game da wannan shawara?

Madam He ta bayyana cewa:

"Ni ba na adawa da wannan, amma wannan ba ya nufin bunkasawa da horar da matasa zai hana raya ababen more rayuwa, wadannan abubuwan suna tafiya ne kafada da kafada, saboda samar da ababen more rayuwa zai bunkasa tattalin arziki da samar da aikin yi ga matasa. Don haka bai kamata a ce a mayar da hankali kan wani bangare guda a bar wani ba."

A karshe, wakilinmu ya tambaye ta, shekaru 4 da suka gabata, Muhammadu Buhari ya ci zabe ne saboda alkawarin da ya yi na yaki da ta'addanci da cin hanci, yaya za ta kwatanta yanayin kasar a yanzu da shekaru 4 da suka gabata?

Madam He ta amsa cewa:

"A gaskiya yanayin tsaro a yanzu ya fi ingantuwa, shekaru 4 da suka wuce, Boko Haram suna kai hare-hare da sace-sacen mutane, amma yanzu ya ragu sosai a arewa maso gabashin kasar, a ganina an samu ci gaba a yaki da ta'addanci. Amma a fannin yaki da cin hanci da rashawa, akwai sauran rina a kaba, wannan ba abu ne da za a samu cikin sauki ba, saboda abu ne da ya dade a kasar da ma nahiyar baki daya, gaskiya ba abu ne mai sauki wajen kawarwa ba."(Fa'iza Mustapha, Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China