in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci kasashen nahiyar da su zage damtse wajen hadewa da ma raya nahiyar
2019-04-10 10:29:09 cri

An yi kira ga kasashen nahiyar Afirka da kungiyoyi shiyyar da ma hukumomin dake nahiyar, da su kara zage damtse a kokarin da ake na dunkulewa da ma raya nahiyar.

Shugaban cibiyar kula da harkokin shugabanci na kungiyar AU Muna Abdalla, shi ne ya yi wannan kiran, gabanin taron shugannin kasashen nahiyar irinsa na farko da zai gudana a tsakiyar wannan shekara. Kiran jami'in ya biyo bayan kokarin shugabannin nahiyar, na cimma nasarar ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063 da shirin shekaru 10 na farko game da shirin raya nahiyar cikin shekaru 50, bayan amincewa da yiwa tsarin gyare-gyare a shekarar 2017.

Abdalla ya jaddada bukatar dake akwai, ta gina al'umma da kyakkyawan tsari a matsayin muhimmin mataki na burin da ake da fatan cimmawa game da raya da kuma bunkasa nahiyar.

Bugu da kari, kasashe 55 mambobin kungiyar AU, suna shirin ganawa irinta ta farko a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

A cewar kungiyar ta AU, ana sa ran taron da zai gudana a tsakiyar wannan shekarar, ya sake fasalta tsare-tsaren tafiyar da harkokin kungiyar. Muhimman batutuwan da ake fatan tattaunawa yayin taron, sun hada da batutuwan siyasa, zaman lafiya da tsaro, da dunkulewar tattalin arziki, da karfafa wakilcin Afirka da magana da murya guda a harkokin kasa da kasa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China