in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An Nada Sabon Sarkin Hausawan Unguwar Asese Ta Jihar Ogun
2019-04-04 16:44:10 cri
Labarin da jaridar Leadership A Yau ta samar a shafinta na internet ya nuna cewa, Sarakunan Gargajiya na al'ummar Hausawa mazauna jihar Ogun a karkashin jagorancin mai martaba Sarkin Hausawan jihar Ogun Alhaji Hasan– Hasan Abeokuta ta nada Alhaji Zakiru Mohmmed Bulanyaki karamar Hukumar Shagari ta jihar Sakkwato a matsayin Sarkin al'ummar Hausawa mazauna unguwar Asese ta karamar hukumar Obafemi Auwode a jihar Ogun, tare da magadansa guda uku. Magaddan sun hada da Alhaji Abubakar Lolo a matsayin garkuwan sarki Hausawa Asese a jihar Ogun da Alhaji Bala Mohammed a matsayin magajin garin Asese da Alhaji Umar Aliyu a matsayin Sarkin Yakin Asese kuma taron nadin sarautar ya gudana ne a cikin makarantar primary ta garin Asese sannan kuma taron ya samu halartar Sarakunan al'ummar Hausawa na jihar Ogun da na Legas da ma'aikata 'yan kasuwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China