in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta dasa itatuwa da bishiyoyi da yawansu ya kai fiye da eka miliyan 18 cikin shekaru 20 da suka gabata
2017-04-06 11:08:29 cri

Bisa labarin da wakilinmu ya samu daga hukumar kula da harkokin gandun daji ta kasar Sin, an ce, bayan da kasar ta kaddamar da aikin gwaji na kare gandun daji a duk fadin kasar ya zuwa yanzu shekaru 20 da suka gabata ke nan, yawan gandun daji da aka dasa ya kai fiye da eka miliyan 18, tare da wasu gandun dajin da ba a dasa su ba, kuma yawansu ya kai fiye da eka miliyan dari 1 da ba a sare su ba.

A shekarar 1998, kasar Sin ta kaddamar da aikin gwaji na kare gandun daji. Sannan a shekarar 2000, ta kaddamar da shirin a duk fadin kasar. Bugu da kari, a shekarar 2016, kasar Sin ta tsai da kudurin daina sare gandun daji domin sayar da su a kasuwa a filayen gandun daji wadanda suke hannun gwamnati. Sakamakon haka, ta yarda da a yi aikin gwaji na daina sare gandun daji a larduna 6 ciki har da lardunan Fujian da Guangxi. Mr. Li Shuming, mataimakin direktan hukumar kula da harkokin gandun daji ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu an riga an canja aikin kare gandun daji, wato za a mai da hankali ne wajen kare yanayin gandun daji maimakon sare su domin samar da katako. Mr. Li ya ce, "Mun sani, kafin a kaddamar da shirin kare gandun daji, muhimmin nauyin da ke bisa wuyan hukumomin gandun daji shi ne samar wa al'umma kayayyakin katako, tare da dasa itatuwa da bishiyoyi domin nuna goyon bayan ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasar. Amma yanzu, an canja nauyin dake bisa wuyanmu, wato yanzu muna kokarin kare yanayin gandun daji maimakon sare su."

Bisa bayanin da aka bayar, an ce, ya zuwa yanzu, yawan gandun daji da kasar Sin take da shi ya kai eka miliyan 208, yawan filayen da itatuwa da bishiyoyi ke shafawa ya kai kashi 21.66 cikin dari bisa jimillar filayen fadin kasar. Ko da yake, bayan da aka kaddamar da shirin kare gandun daji, wannan adadi ya karu cikin sauri, amma idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, wannan adadi ya yi kadan. Sakamakon haka, Mr. Li Shuming ya bayyana cewa, hukumar kula da harkokin gandun daji ta kasar Sin za ta kara mai da hankali kan kyautata ingancin gandun daji a nan gaba. Alal misali, za a yi kokarin gyara filayen gandun daji inda wasu itatuwa da bishiyoyi suka yi kusan mutuwa, sannan za a yi kokarin kyautata amfanin gandun daji wajen kare muhallin duniyarmu. Bugu da kari, kasar Sin za ta yi namijin kokari wajen dasa itatuwa da bishiyoyi iri daban daban domin kara ire-iren itatuwa da bishiyoyi da kasar Sin take da su yanzu. Mr. Li Shuming ya kara da cewa, "Ya zama dole mu yi kokarin kyautata ingancin gandun daji. Yanzu, a kowace eka, yawan itatuwa da bishiyoyi da muke da su ya kai kubik mita 89. A hakika dai, wannan adadi bai yi yawa ba. Dole ne mu yi kokarin kara yawan itatuwa da bishiyoyi masu inganci da ake dasa su a kowace eka."

Bisa bayanin da Mr. Li Shuming ya yi, an ce, ya zuwa shekara ta 2030, yawan itatuwa da bishiyoyin da za a dasa a kowace eka zai karu fiye da kashi 30 cikin dari. Sannan a lokacin da ake kokarin kyautata ingancin gandun daji, hukumar kula da harkokin gandun daji ta kasar Sin za ta kara mai da hankali wajen kare gandun daji, da kuma kyautata ko fitar da dokokin kare gandun daji. Li Shuming ya bayyana cewa, "Yaya za mu yi a nan gaba? Tabbas ne za mu yi kokarin gyara fuska ga tsarin aikinmu da kuma kara mai da hankali wajen tsara wani babban shirin karewa da kuma kyautata ingancin gandun daji. Abin da za mu yi yanzu shi ne gyara 'ka'idojin kare gandun daji', inda za mu tabbatar da matakan da za mu dauka, da abubuwan da bai kamata a yi ba a bayyane. Sakamakon haka, za a iya fitar da wata dokar kare gandun daji. Sannan kuma, yanzu muna gyara 'dokar gandun daji'."

Bisa bayanin da hukumar kula da harkokin gandun daji ta kasar Sin ta bayar, an ce, a nan gaba, kasar Sin za ta kara kyautata ingancin filayen da suke dacewa da dasa itatuwa da bishiyoyi, ta yadda za a iya tabbatar da cewa, nan da shekara ta 2030, yawan filayen itatuwa da bishiyoyi zai karu da eka miliyan 3. Karfin yin watsi da sinadarin dumama yanayin duniya zai karu fiye da kashi 30 cikin dari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China