Birnin Wuhan, wanda ya kasance sanannen waje ne dake yankin Yangtze River, kuma kogin Han dake ratsa birnin ya kasance karamin kogi mafi tsawo na kogin Yangtze, yana da girman kasa mai dausayi kimanin kilomita 1,624, kuma ya kwashe kusan kashi 18.9 bisa 100 na adadin yankunan birnin. Hukumar ta sanar da cewa, yankin dausayi na Wuhan ya zamanto gida ne ga wasu nau'ikan dabbobin daji sama 400 kana akwai wasu nau'ikan tsirrai sama da 400 a yankin.
"Wuhan yana da karfin da zai iya yin takara ba wai saboda dunbun albarkatun yankuna masu dausayi da yake da shi kadai ba, har ma saboda yadda ya kasance yanki na farko dake da wasu dabaru na musamman wajen kare wurare masu ni'ima," in ji Lei Gang, wani kwararren masanin asusun kula da dabbobin daji na duniya (WWF) na shirin kyautata tsabtar ruwa na kasar Sin.
Ramsar Convention, ko kuma Convention on Wetlands, wata yarjejeniya ce tsakanin gwamnatoci wacce aka amince da ita tun a shekarar 1971. Yarjejeniyar ta samar da wani shiri na kasa da kuma tsarin hadin gwiwa na kasa da kasa game da batun kiyayewa da kuma yadda za'a yi amfani da wurare masu dausayi da albarkatun dake cikinsu yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)