in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasashen dake kudu da Sahara zai bunkasa da kaso 2.3 a 2018
2019-04-09 09:13:01 cri

Wani rahoton da bankin duniya ya fitar jiya Litinin a birnin Nairobin kasar Kenya, ya yi hasashen cewa, bunkasar tattalin arzikin kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara za ta ragu zuwa kaso 2.3 cikin 100 a shekarar 2018 daga kaso 2.5 cikin 100 a shekarar 2017.

A cewar rahoton, raguwar da ba a yi zato ba, kan baki dayan ci gaban tattalin arzikin, ya nuna rashin tabbas da duniya ke fuskanta a halin yanzu, da rashin daidaiton tattalin arzikin kasashen nahiyar, ciki har da yadda aka gaza kula da basussuka, da hauhawar farashin kayayyaki gami da gibin cinikayya.

Bincike ya nuna cewa, koma bayan tattalin arzikin kasashen nahiyar ta Afirka dake kudu da hamadar Sahara, ya fi kamari ne a watanni shida na farkon shekarar 2018, ya kuma nuna tasirin rashin shigo da kayayyaki daga manyan kasashen yankin dake fitar da mai kamar kasashen Najeriya da Angola, sakamakon rashin hako man biyo bayan tashin farashin man a kasuwannin duniya.

Haka kuma binciken ta yi nuni da cewa, hadarin dake tattare a wasu kasashe kalilan, ya sanya rabi cikin kasashen nahiyar dake yankin kudu da hamadar Sahara, asarar kaso 0.5 cikin dari na ci gaban da suke samu a shekara, wadda ya kai kusan kaso 2.6 cikin dari na alkaluman ci gaban sama da shekaru biyar. Sai dai kuma binciken ya yi hasashen cewa, ci gaban yankin, zai kai kaso 3.3 cikin 100 a shekarar 2020.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China