Bankin duniya ya sanar da cewa, zai taimakawa kasar Sudan wajen tunkarar kalubalen tattalin arziki a bangaren kula da harkokin kudi da tsara tattalin arziki.
Wata tawaga daga bankin, ta tattauna a jiya Lahadi, da ministan kudin kasar Mohamed Osman Al-Rikabi, a Khartoum, babban birnin Sudan.
Wakilin bankin duniya a Sudan Adama Coulibaly, ya shaidawa manema labarai cewa, biyo bayan tattaunawar, bankin duniya ya kuduri niyyar kara adadin ayarinsa masu kula da tattalin arzki a Sudan, tare da karfafa hadin gwiwa da gwamnatin kasar. (Fa'iza Mustapha)