in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ingantacciyar Shinkafar "GSR" ta kasar Sin ta inganta ci gaban aikin gona a nahiyoyin Asiya da Afrika
2019-04-03 11:04:54 cri
Masana kimiyyar aikin gona na kasar Sin, sun samar da wasu sabbin nau'ikan shinkafa masu inganci da ake kira "Green Super Rice ko (GSR)" a takaice, ga kasashen Asiya da Afrika masu tasowa, domin rage yunwa da karawa manoma kudin shiga.

Aikin da aka kadamar tun shekarar 2008, bisa goyon bayan Gwamnatin kasar Sin da Gidauniyar Mill and Melinda Gates, wanda ya samar da nau'ikan shikafa 78 da aka noma kan gona mai fadin kadada miliyan 6.12 domin kasashe 18, na sa ran amfanawa kananan manoman shinkafa miliyan 30 a nahiyoyin Asia da Afrika.

A cewar Li Zhikang, mai bincike a kwalejin nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin, nau'ikan na shinkafar GSR ingantattu ne da za su iya samar da amfanin gona mai yawa sosai. Sannan ba sa bukatar takin zamani da maganin kashe kawari da ruwa mai yawa, domin suna iya jure kwari da cututtuka da fari da sauran wasu abubuwa masu barazana ga noman shinkafa.

Inda ake sa ran amfani da su sun hada da kasashe 9 na nahiyar Asiya da wasu 9 na nahiyar Afrika da suka hada da Mozambique da Tanzania da Rwanda da Liberia da Habasha da Uganda da Nigeria da Mali da kuma Senegal. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China