Dr. Wang Shimei ta cibiyar nazarin aikin gona ta lardin na Anhui ta bayyana cewa, a shekarar 2009 ne aka fara fitar da irin shinkafar zuwa kasar Angola. Kuma tun daga wancan lokacin zuwa yanzu, yawan shinkafar da ake nomawa a kasar ya kai eka 10,000.
Wang ya ce, a watan Yunin wannan shekara wasu kwararru a fannin aikin gona daga kasashe 10, ciki har da kasashen Masar da Uganda, sun zo nan kasar Sin don nazarin dabarun noma irin shinkafar, inda suke fatan zai taimaka wajen kara samun yabanya a kasashensu, sakamakon farin da suke fuskanta.
Bayanai na nuna cewa, ana noma irin wannan shinkafa a kasashen kamar Philippines da Cambodia da Pakistan da kuma Kamaru.(Ibrahim)