Ma'aikatar man fetur da hakar ma'adinai ta kasar ta fada cikin sanarwar cewa, yankunan masu albarkatun mai na El-Nar, El-toor da Manga, dukkan yankunan suna arewacin kasar ne za su fara aikin hako man daga ranar 27 ga watan Afrilu, tare ta alwashi hako gangar danyen mai 70,000 a kullum zuwa watan Yuni.
Wannan matakin ya biyo bayan wani rangadi ne da ministan albarkatun mai na Sudan Ezekiel Lol Gatkuoth da takwaransa na kasar Sudan Ishag Adam Bashir Gamaa suka kai zuwa yanki mai arzikin mai na kasar a ranar Asabar.
Gatkuoth ya bukaci kamfanin hakar mai na kasar, wanda ke gudanar da aikin gyaran rijiyoyin mai na El-Nar da El-toor, da ya gaggauta kammala aikin domin cimma wa'adin da aka diba na dawo da aikin hakar man a ranar 27 ga watan Afrilu.
Ministocin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar amincewa don baiwa kamfanonin dake aikin hakar man a Sudan ta kudu da su yi amfani da yankunan kasar Sudan wajen yin jigilar kayayyakin aikin hako albarkatun man. (Ahmad Fagam)